Akalla manoma 550 ne suka amfana da talalfini irin shuka da Gwamnatin Tarayya ta raba wa manoman da suka fito daga Kananan Hukumomi biyar a Jihar Gombe.
Daraktan Ayyukan Bunkasa Harkokin Noma na Jihar Gombe (GADP), Joseph Hussaini ne ya bayyana haka da ya ke zantawa da manema labarai a Gombe, ranar Laraba.
Hussaini ya ce talalfin an raba shi ne domin a rage wa manoma radadin kuncin matsin tattalin arzikin da suka shiga a sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus.
Ya ce an karbi irin shukar a cikin watan Yuli, kuma nan da nan aka raba shi da manoman, musamman ganin cewa wasu manoman har sun yi nisa da fara aikin daminar bana, shi ya sa ba a bata lokaci wajen rabon kayan irin shukar ba.
Ya ce Ma’aikatar Harkokin Noma da Bunkasa Yankunan Karkara ta Tarayya ce ta raba kayan irin, ta hannun Cibiyar Binciken Irin Shuke-shuke na Yankin Afrika (ICRISAT).
Ya ce an raba musu irin shuka daban-daban da suka hada har da gero da sauran su.
“Kananan Hukumomin da suka amfana sun hada da Yamaltu-Debba, Nafada, Shongom, Balanga da Dukku.” Inji Joseph.
Ya ce an kasa irin da sunan kowane aka bai wa tallafin, kowace Karamar Hukuma muttum 110.
Ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa wannan kokarin raba wa manoma irin shuka da ta yi a lokacin da suke halin matsin rayuwa sakamakon cutar Coronavirus da ta barke.