Mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Rasha Oleg Grinev ya bayyana cewa maganin rigakafin Korona da kasar ta hada na matakin gwaji na karshe kafin fara amfani da shi.
Grinev ya ce gwamnati na kokarin yi wa maganin rajista cikin mako mai zuwa.
” Ina tabbatar da cewa maganin warkar da cutar Korona na da ingancin warkar da cutar a jikin mutum.
Wani cikin masana kimiyya da suka hada maganin ya ce suna sa ran fara sarrafa maganin da yawa a watan Satumba.
Hukumar gudanar da bincike ‘Gamaleya Research Institute for Epidemiology and Microbiology’ ce ta hada wannan magani.
Hukumar ta gwada inganci da sahihancin aikin maganin a jikin wasu ma’aikatan gwamnati da sojoji.
Sakamakon gwajin ya nuna cewa rigakafin ya warkar da cutar a jikin wadannan mutane ba tare da sun Samu matsaloli ba.
Ma’aikatar tsaro ta kasar ta ce duk sojoji da aka bai wa wannan magani sun warke ba tare da an samu wasu matsaloli ba.
Idan ba a manta ba ranar 4 ga Agusta Shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa wasu magungunan da aka hada suna wurin gwaji tukunna. Ya ce uku daga cikin samfuri hudu dakr dakin gwaji na mataki uku.
Sai dai Ghebreyesus ya ce har yanzu babu wani magani kaifi-daya a duniya da ke warkar da cutar Coronavirus ko hana ta watsuwa da fantsama.
Ya ce kula da lafiya da tsaftar jiki da ta muhalli da kuma aikin dakile cutar su ne mafi muhimmanci a yanzu.
A yanzu fadada aikin gwaji da bayar da magani da gano wadanda aka dauki cutar a jikin su, shi ne abin da za a fi maida hankali.