KORONA: An samu karin mutum 593 ranar Laraba da suka kamu, Najeriya ta zarce mutum 50,000

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 593 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –172, Filato-186, FCT-62, Oyo-27, Delta-25, Rivers-20, Ondo-19, Edo-18, Kaduna-17, Enugu-12, Akwa Ibom-10, Ogun-7, Abia-6, Gombe-6, Kano-3 da Osun-3

Yanzu mutum 50,488 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 37,304 sun warke, 985 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,199 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 17,092 FCT –4,837, Oyo – 3007, Edo – 2,475, Delta –1,671, Rivers 2,027, Kano –1,683, Ogun – 1,587, Kaduna –1,882 Katsina –746, Ondo –1,482 , Borno –706, Gombe – 684 , Bauchi – 607, Ebonyi – 943, Filato -2,043, Enugu – 1,025, Abia – 713, Imo – 506, Jigawa – 322, Kwara – 913, Bayelsa – 352, Nasarawa – 386, Osun – 757, Sokoto – 154, Niger – 232, Akwa Ibom – 260, Benue – 430, Adamawa – 185, Anambra – 181, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 206 , Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 77.

Kasar Jamus za ta yi wa ‘yan kasarta kaf rigakafin Korona daga nan zuwa 2021

Shugaban hukumar tantance sahihanci da ingancin maganin rigakafi na kasar Jamus Klaus Cichutek ya bayyan cewa nan ba da dadewa ba kasar za ta kammala hada maganin rigakafin Korona da za ta yi wa ‘yan kasar Kaf, daga nan zuwa 2021.

Da yake zantawa da jaridar ‘Funke group of newspapers’ Cichutek ya ce sakamakon gwajin maganin rigakafin cutar Korona na farko da na biyu da masana suka yi a kasar ya nuna cewa maganin na da ingancin warkar da cutar kwatakwata a jikin wanda ya kamu.

Idan ba a manta ba a watan Agusta ne kasar Rasha ta bayyana cewa masana magunguna a kasar sun kammala hada rigakafin Korona da kowa zai yi amfani da shi.

Shugaban kasar Vladimir Putin ya ce Masana kimiyar dake hukumar gudanar da bincike ‘Gamaleya Institute’ dake Moscow ne suka hada wannan magani na rigakafi bayan akalla watanni biyu suka yi suna gwajin inganci da sahihancin sa.

Ya ce yana sa ran nan ba da dadewa ba za a fara sarrafa maganin da yawa domin mutanen kasar.

Yanzu kasar Rasha ita ce kasa ta farko da ta fara hada maganin rigakafin cutar Korona da hakan zai taimaka wajen rage yawan mace-macen da ake samu a kasar sanadiyyar wannan cuta.

Share.

game da Author