KORONA: An samu karin mutum 340 ranar Juma’a da suka kamu, Mutum 51,304 sun Kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 340 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 33, Kaduna-63, FCT-51, Filato-38, Delta-25, Gombe-21, Adamawa-21, Edo-20, Katsina-17, Akwa Ibom-11, Ekiti-10, Rivers-9, Ondo-5, Ebonyi-4, Cross River-3, Ogun-3, Sokoto-2, Imo-2 da Nasarawa-2

Yanzu mutum 51,304 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 37,885 sun warke, 996 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,423 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 17,360 FCT –4,932 , Oyo – 3,017, Edo –2,508, Delta –1,696, Rivers 2,048, Kano –1,692, Ogun – 1,594, Kaduna –1,986 Katsina –768, Ondo –1,487 , Borno –739, Gombe – 709, Bauchi – 607, Ebonyi – 947, Filato -2,109, Enugu – 1,030, Abia – 726, Imo – 519, Jigawa – 322, Kwara – 920, Bayelsa – 352, Nasarawa – 389, Osun – 757, Sokoto – 156, Niger – 232, Akwa Ibom – 260, Benue – 430 , Adamawa – 206, Anambra – 181, Kebbi – 90, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 216 , Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 80.

Gwamnatin Kaduna ta janye dokar hana salloli biyar na kullum a masallatan jihar

Gwamnatin Kaduna ta janye dokar hana salloli biyar na kullum a masallatan jihar. Suma coci-coci dake gudanar da Ibada a kullum an basu damar bude wa don cigaba da ibada.

Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar ta saka dokar hana salloli biyar a fadin jihar tun bayan barkewar annobar Korona a duniya.

Mai ba gwamnan Kaduna Shawara kan yada labarai, Muyiwa Adekeye ya shaida haka a wata gajeruwar sanarwa da ya fitar ranar Juma’a cewa an yanke shawarar yin hakane bayan an gudanar da taro tsakanin malaman addinin Musulunci da na Kirista da kuma jami’an lafiya a jihar.

Ya ce za a ci gaba da salloli a masallatai da yin Ibada a Coci Coci sai dai dole za arika bin dokokin kariya daga Korona a wuraren ibadun a koda yaushe.

Sassauta doka don yin Sallar Juma’a

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sassauta dokar hana bude wuraren kasuwanci da sauran wuraren mua’muloli a jihar.

El-Rufai ya amince musulmai su rika sallar Juma’a sannan Kiristoci su rika fita zuwa ibada a coci ranar Lahadi.

Baya ga haka ba a amince a rika yin salloli biyar da aka saba ba, kuma makarantu da manyan kasuwannin jihar duk za su ci gaba da zama a garkame sai bayan an sake yibwa dokar garambawul.

Bayan haka matafiya daga kananan hukumomin jihar Kaduna za su iya ci gaba da shiga da fice daga garuruwa.

Duk wuraren kasuwanci da zasu bude, su tabbata sun samar da na’urar gwajin yanayin zafin jikin mutum, ruwan wanke hannaye, da man tsaftace su.

Haka kuma suma Otel a fadin jihar duk za su iya budewa domin ci gaba da ayyuka, saidai kuma dole su kiyaye dokokin da aka saka ne.

Suma ma’aikatan gwamnati za su dawo aiki kamar yadda shugaban ma’aikatan jihar za ta sanar nan gaba.

Sannan kuma gwamnati ta ce a hankali za ta ci gaba da tattaunawa da shugabannin kasuwanni da makarantu domin tsara yadda za a bude su ba tare da an samu matsala ba.

Share.

game da Author