Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 304 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -59, FCT -90, Ondo-39, Taraba-18, Rivers-17, Borno-15, Adamawa-12, Oyo-11,Delta-9, Edo-6, Bauchi-4, Kwara-4, Ogun-4, Osun-4, Bayelsa-3, Filato-3, Niger-3, Nasarawa-2 da Kano-1.
Yanzu mutum 44,433 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 31,851 sun warke, 910 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,673 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,414 FCT – 4,087, Oyo – 2,782, Edo – 2,317, Delta –1,529, Rivers 1,859, Kano –1,598 , Ogun – 1,411, Kaduna – 1,498, Katsina –746, Ondo – 1,243 , Borno –628, Gombe – 620, Bauchi – 565, Ebonyi – 808, Filato – 1,243, Enugu – 846, Abia – 602, Imo – 469, Jigawa – 322, Kwara – 790, Bayelsa – 342, Nasarawa – 356, Osun – 584, Sokoto – 153, Niger – 226, Akwa Ibom – 221, Benue – 356, Adamawa – 176, Anambra – 135, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 152, Taraba- 72, Kogi – 5, da Cross Rivers – 58.
Rahoton watan Agusta da Hukumar Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta first ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ba su da wata mu’amala da kusanci da wanda ya fita kasar waje, ko wata jiha ko kusanci da mai cutar Coronavirus.
Hakan ya na nufin akasarin wadanda suka kamu a Najeriya, ba su san ta yadda aka yi suka kamu ba.
Duk da raguwar yawan rahotannin adadin masu kamuwa da cutar Coronavirus ke yi a kullum a yanzu, har yau akwai fargabar cewa sake bude harkokin komai a kasar nan a yanzu zai iya zama sammakon-bubukuwa.