Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 354 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 76, FCT-78, Kaduna-23, Ebonyi-19, Oyo-18, Nasarawa-17, Rivers-17, Delta-16, Kwara-15, Akwa Ibom-13, Edo-12, Ogun-12, Filato-11, Kano-9, Bauchi-6, Borno-6 da Ekiti-6
Yanzu mutum 45,244 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 32,430 sun warke, 930 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,884 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,627 FCT – 4,241, Oyo – 2,825, Edo – 2,340, Delta –1,557, Rivers 1,912, Kano –1,608 , Ogun – 1,428, Kaduna – 1,530, Katsina –746, Ondo – 1,243 , Borno –634, Gombe – 620, Bauchi – 574, Ebonyi – 838, Filato –1,294, Enugu – 880, Abia – 625, Imo – 472, Jigawa – 322, Kwara – 815, Bayelsa – 342, Nasarawa – 360, Osun – 586, Sokoto – 154, Niger – 226, Akwa Ibom – 324, Benue – 356, Adamawa – 176, Anambra – 142, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 159, Taraba- 72, Kogi – 5, da Cross Rivers – 68.
Yadda Korona ta gurgunta karatun Yara biliyan 1 a duniya
Idan ba a manta ba a cikin wanna watan Agusta ne Shugaban majalisar dinkin duniya UN Antonio Guterres ya koka kan yadda annobar Korona ta gurgunta karatun yara a fadin duniya.
Guterres Ya ce annobar Korona ya gurgunta yanayin karatun yaran duniya da ba a taba ganin irin sa ba.
Ya ce kafin bayyanan Korona yara sama da miliyan 250 basu zuwa makaranta a fadin duniya. A dalilin wannan cuta ta Korona sai yawan yaran ya karu don ko ya zarce mutum biliyan 1.
Guterres ya Kuma ce amfani da yanar gizo da sauran na’urorin fasaha da ake yi domin ilimantar da yara yayi matukar tasiri sosai sai dai kuma yaran talakawa da kasashen da basu da cigaba irin na yanar gizo, wadanda ke sansanonin ‘yan gudun hijira, da nakasassu duk sun fada cikin matsalar rashin samun ilmi.
Ya ce a dalilin haka wadannan yara sun fantsama cikin matsalolin da ya hada da yi wa yara auren wuri, rashin cin abincin dake karfafa garkuwa jiki, rashin daidaita jinsin Masa da Mata da dai sauran su.
Bude makarantu, Kara ware wa fannin ilimi kudade, Kai wa yaran dake kauyuka ilimin boko sannan da amfani da dabarun koyarwa na zamani a kauyuka domin yaran dake karkara su amfana na cikin hanyoyin da za su taimaka wajen farfado da fannin ilimi a wannan lokaci da ake fama da annobar Korona a Duniya.