Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 453 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –71, FCT-75, Benue-53, Delta-39, Borno-30, Enugu-25, Filato-24, Osun-20, Abia-19, Oyo-17, Kaduna-16, Kano-13 Ebonyi-13, Ogun-9, Kwara-7,, Ondo-6, Gombe-3, Ekiti-2, Akwa Ibom-1 da Rivers-1
Yanzu mutum 46,140 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 33,044 sun warke, 942 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,154 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 15,768 FCT – 4,376, Oyo – 2,860, Edo – 2,376, Delta –1,596, Rivers 1,939, Kano –1,622, Ogun – 1,439, Kaduna – 1,566, Katsina –746, Ondo – 1,284 , Borno –682, Gombe – 629, Bauchi – 576, Ebonyi – 851, Filato –1,421, Enugu – 905, Abia – 644, Imo – 476, Jigawa – 322, Kwara – 833, Bayelsa – 346, Nasarawa – 367, Osun – 625, Sokoto – 154, Niger – 226, Akwa Ibom – 235, Benue – 409, Adamawa – 185, Anambra – 142, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 161, Taraba- 72, Kogi – 5, da Cross Rivers – 68.
Akasarin ‘yan Najeriya da suka kamu da Korona, ba su san daga wanda suka dauki cutar ba.
Mafi yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ba su da wata mu’amala da kusanci da wanda ya fita kasar waje, ko wata jiha ko kusanci da mai cutar Coronavirus. Hakan ya na nufin akasarin wadanda suka kamu a Najeriya, ba su san ta yadda aka yi suka kamu ba.
Wannan na cikin rahoton watan Agusta da Hukumar Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta fitar a ranar Lahadin a Abuja.
Duk da raguwar yawan rahotannin adadin masu kamuwa da cutar Coronavirus ke yi a kullum a yanzu, har yau akwai fargabar cewa sake bude harkokin komai a kasar nan a yanzu zai iya zama sammakon-bubukuwa.