KORONA: Abuja 44, Kaduna 41, Najeriya ta zarce mutum 50,000 da suka kamu

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 476 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –235,FCT-44, Kaduna-41, Borno-33, Filato-28, Abia-13, Edo-13, Rivers-12, Imo-11, Oyo-10, Kano-9, Kwara-7, Enugu-5, Katsina-5, Gombe-4, Ogun-4, Nasarawa-1 da Zamfara-1

Yanzu mutum 50,964 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 37,569 sun warke, 992 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 12,403 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 17,327 FCT –4,881, Oyo – 3017, Edo –2,488, Delta –1,671, Rivers 2,039, Kano –1,692, Ogun – 1,591, Kaduna –1,923 Katsina –751, Ondo –1,482 , Borno –706, Gombe – 688 , Bauchi – 607, Ebonyi – 943, Filato -2,071, Enugu – 1,030, Abia – 726, Imo – 517, Jigawa – 322, Kwara – 920, Bayelsa – 352, Nasarawa – 387, Osun – 757, Sokoto – 154, Niger – 232, Akwa Ibom – 260, Benue – 430, Adamawa – 185, Anambra – 181, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 67, Ekiti – 206 , Taraba- 78, Kogi – 5, da Cross Rivers – 77.

Birtaniya ta kirkiro na’urar yin gwajin Korona cikin sauki

Gwamnatin Birtaniya ta kirkiro na’urar da zai taimaka wajen gano alamu tare da yi wa mutane gwajin Korona cikin sauki.

Gwamnati ta ce za ta gwada ingancin na’urar a ranar Alhamis din makon jiya a jikin mutanen da suka mika kansu domin haka sannan da wasu mazaunan wuraren Isle of Wight da London borough of Newham.

A cikin kwanaki biyar mutum miliyan 1 sun kamu, 50,000 sun mutu a duniya.

A cikin kwanakin biyar duniya ta samu karin mutum miliyan 1 da suka kamu da cutar Covid-19.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar a ranar Lahadi cewa Mutum miliyan 20 ne ke dauke da cutar a duniya.

Sai dai a ranar Alhamis din da ya gabata adadin yawan ya karu zuwa Mutum miliyan 21.

Bisa ga sakamakon binciken ‘Worldometers’ mutum 200,000 sun kamuwa da cutar a tsakanin kwanaki biyar da suka wuce a duniya.

Kuma a cikin wadannan kwanaki biyar mutum 50,000 sun mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar da hakan ya kawo adadin yawan mutanen da suka mutu a duniya ya kai 750,000.

Har Yanzu dai kasar Amurka ce kan gaba wajen wadanda suka fi kamuwa da cutar a duniya. Daga nan sai kasashen Rasha, Brazil

Cutar ta yadu zuwa Turai, Amurka, Asia da yankin kudancin Amurka da Afrika ta kudu.

Share.

game da Author