A cikin kwanakin biyar duniya ta samu karin mutum miliyan 1 da suka kamu da cutar Covid-19.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar a ranar Lahadi cewa Mutum miliyan 20 ne ke dauke da cutar a duniya.
Sai dai a ranar Alhamis adadin yawan ya karu zuwa Mutum miliyan 21.
Bisa ga sakamakon binciken ‘Worldometers’ mutum 200,000 sun kamuwa da cutar a tsakanin kwanaki biyar da suka wuce a duniya.
Kuma a cikin wadannan kwanaki biyar mutum 50,000 sun mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar da hakan ya kawo adadin yawan mutanen da suka mutu a duniya ya kai 750,000.
Har Yanzu dai kasar Amurka ce kan gaba wajen wadanda suka fi kamuwa da cutar a duniya. Daga nan sai kasashen Rasha, Brazil
Cutar ta yadu zuwa Turai, Amurka, Asia da yankin kudancin Amurka da Afrika ta kudu.
Tsananta yin gwajin Korona
Kwararrun ma’aikatan lafiya sun bayyana cewa duniya ta samu karin mutum miliyan daya ne a dalilin tsananta gwajin cutar da kasashen duniya suka yi.
Masana sun ce a kasar Amurka mutum zai iya garzaya asibiti ko shagon saida da magani don yin gwajin cutar cikin sauki sai dai har yanzu akan dade kafin mutum ya samu sakamakon gwajin cutar.
Daga cikin mutum miliyan 200 Najeriya gwamnati ta yi wa mutum 340,000 gwajin cutar.
Domin inganta yin gwajin cutar Najeriya ta ware naira miliyan 8.49 domin siyo na’urorin gwajin cutar.
Kasashen da suka fi fama da Korona a duniya
Zuwa Yanzu mutum miliyan 21, 099, 879 ne suka kamu da cutar, mutum 757, 997 sun mutu a duniya.
Kasar Amurka – mutum miliyan 5.4 da suka kamu, mutum 170,000 sun rasu.
Kasar Brazil – mutum miliyan 3.2 da suka Kamu, mutum miliyan 2.4.
Mutum 900,000 sun kamu da cutar a kasar Rasha, Afrika ta Kudu – mutum 550, 000.
Zuwa Yanzu mutum miliyan 6,393,193 na kwance a asibiti, mutum 13, 948, 689 sun warke a duniya.