Kotu a jihar Kano ta aika da wata mata mai Suna Saratu Ya’u asibitin mahaukata domin a tabbatar bata da tabuwar hankali.
Kotun na tuhumar Saratu dake zama a kauyen Sabon Birni karamar hukumar Gwarzo bisa laifin kisan kai.
Lauyan da ya shigar da karar Lamido Soron-Dinki ya ce Saratu ta aikata kisa kai ranar 12 ga Yunin 2018 a gidanta dake Sabon Birni, Gwarzo.
Sorondinki ya ce a wannan rana da misalin karfe 8:25 Saratu ta yi wa dan da ta haifa mai shekaru biyar yankan rago.
Ya yi kira ga kotun da ta yi amfani da dokar jihar na shekara ta 2019 domin a aika da Saratu a asibitin mahaukata domin tabbatar da lafiyar kwakwalwar ta.
Saratu ta amsa laifin da ta aikata.
Alkalin kotun ya yanke hukuncin a kai Saratu asibitin mahaukata domin a duba ta sannan za a ci gaba da shari’a ranar 8 ga watan Oktoba.
Idan ba a manta ba a cikin wannan mako ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama matar da ta daure dan kishiyarta a wani daki har na tsawon shekara 15.
Kakakin rundunar Abdullahi Haruna ya sanar da haka yana mai cewa matar da mijinta wato mahaifin yaron sun daure yaron a cikin gidan su dake kwatas din Sheka a karamar hukumar Kumbotoso a cikin wani gurbataccen daki babu ruwa babu abinci.
Ya ce jami’an tsaro sun ceto Ibrahim Lawan mai shekaru 40 daga cikin wannan mummunar hali ranar 16 ga watan Agusta.