Kashi 70% na kudaden da gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka raba a watan Yuli na haraji ne, ba kudin fetur ba ne – FIRS

0

An bayyana cewa kashi 70% na kudaden da gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka raba a watan a watan Yuli, duk daga harajin da ake tatsa ne daga nan cikin gida Najeriya, ba na ribar danyen man fetur ba ne.

Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida ta Kasa (FIRS) ta bayyana a ranar Litinin a Abuja.

Shugaban Hukumar, Muhammad Nami ya ce da ya ke fantsama da barkewar cutar Coronavirus ta gurgunta hanyoyin tattalin arzikin kasa da dama, sai ya kasance duk akasarin kudaden da ake tafiyar da Najeriya, daga harajin da ake karba ake samun su.

Nami ya yi wannan bayani a wani shirin Kaakaki da gidan talbijin na AIT ke shiryawa a ranar Litinin.

Shirin ya yi shi ne matsayin kokarin wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin kiyayewa da kuma nuna da’ar biyan haraji a kan kari ga gwamnatin tarayya.

“An raba naira bilyan 696 a zaman Majalisar Zartaswa a watan Yuli tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi.

“Kashi 3O bisa 100 ne kadai aka tara daga ribar danyen man fetur da harajin da kwastan ke karba na shigo da kaya daga kasashen ketare.

“Amma kashi 70 bisa 100 na wadannan kudaden duk dagan cikin gida muka tara su, daga harajin cikin gida da mu ke tarawa. Kwatankwacin kudaden da muka tara din aka raba a Yuli sun kai kusan naira bilyan 500, daga hanyoyin tara kudade daban-daban, ciki har da ‘Harajin Kudin La’adar Gwamnati’, wato stamp duty.” Inji Nami.

Daga nan ya yi kira ga daidaikun ‘yan Najeriya da kuma kamfanoni su rika biyan harajin da ya wajaba a kansu a kan kari.

“Babu mai son biyan haraji duk kuwa da cewa kiwa ya san biyan haraji wajibi ne. Shi biyan haraji a kowane lokaci abu ne Mai matukar muhimmanci.

Najeriya za ta yamutse idan ba a biyan haraji – Shugaban FIRS

Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida ta Kasa (FIRS), Muhammad Mani, ya yi kakakusan gsrgadi cewa idan jama’a suka ki, ko suka daina biyan harajin cikin jida, to Najeriya za ta harmutse, saboda za a rasa isassun kudaden da za a gudanar wa kasa manyan ayyuka.

Nami, wanda ya yi amfani da kalmar “chaos” ya fassara halin da Najeriya za ta za shiga idan ba a biyan haraji, ya bayyana cewa haraji ne ya ceci kasar nan yayin da cutar Coronavirus ta dagargaji kasashen duniya, kuma dimbin na jama’a na rasa ayyuakn su.

Da ya koma kan harajin Harajin La’adar Gwamnatin Tarayya (stamp duty), Nami ya ce ba wani abin tayar da hankali ba ne, kuma ba sabon abu ba ne, saboda masu hulda da bankuna na biyan kudaden a cakin kudin da suke amfani da shi, tun daga 1939 shekarar da aka kirkiro shi a Najeriya.

Share.

game da Author