A ranar Talata ne Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa masana magunguna a kasar sun kammala hada rigakafin Korona da kowa zai yi amfani da shi.
Masana kimiyar dake hukumar gudanar da bincike ‘Gamaleya Institute’ dake Moscow ne suka hada wannan magani na rigakafi bayan akalla watanni watanni biyu suka yi suna gwajin inganci da sahihancin sa.
Putin ya tabbatar da inganci da sahihancin maganin yana mai cewa daya daga cikin ‘ya’yansa da ta kamu da cutar ta samu lafiya bayan ta yi amfani da rigakafin.
Ya ce yana sa ran nan ba da dadewa ba za a fara sarrafa maganin da yawa domin mutanen kasar.
Yanzu kasar Rasha ita ce kasa ta farko da ta fara hada maganin rigakafin cutar Korona da hakan zai taimaka wajen rage yawan mace-macen da ake samu a kasar sanadiyyar wannan cuta.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Rasha Oleg Grinev ya bayyana cewa maganin rigakafin Korona da kasar ta hada na matakin gwaji na karshe kafin fara amfani da shi.
Grinev ya ce gwamnati na kokarin yi wa maganin rajista cikin mako mai zuwa.
Wani cikin masana kimiyya da suka hada maganin ya ce suna sa ran fara sarrafa maganin da yawa a watan Satumba.
Hukumar gudanar da bincike ‘Gamaleya Research Institute for Epidemiology and Microbiology’ ce ta hada wannan magani na rigakafin Korona.
Hukumar ta gwada inganci da sahihancin aikin maganin a jikin wasu ma’aikatan gwamnati da sojoji.
Sakamakon gwajin ya nuna cewa rigakafin ya warkar da cutar a jikin wadannan mutane ba tare da sun samu matsaloli ba.