Kamuwa da Korona ba ya hana Uwa ta shayar da dan ta nono – WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa mace dake dauke da kwayoyin cutar Korona za ta iya shayar da danta nono yadda ya kamata ba tare da jaririn ya kamu da cutar ba.

WHO ta ce muddun Uwa ta kiyaye dokokin kare kai daga kamuwa da cutar Korona, to dan ta ba zai kamu ba don ta shayar dashi.

Kungiyar ta fadi haka ne domin karfafa gwiwowin mata wajen shayar da ‘ya’yan su nono akalla na tsawon watanni shida.

Idan ba a manta ba a a makon da ya gabata ne aka yi taron tunawa da mahimmancin shayar da jariri nonon uwa na shekarar 2020 inda Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya UNICEF suka yi kira ga mata uwaye su juri shayar da ‘ya’yan su nono koda sun kamu da Korona.

Kungiyoyin biyu sun ce sakamakon bincike ya nuna cewa mace dake dauke da kwayoyin cutar Korona na iya shayar da danta nono ba tare da dan ya kamu da cutar ba.

Kungiyoyin sun ce yin wannan kira a Wannan lokaci da duniya ke yaki da annobar Korona na da muhimmancin gaske ganin yadda kamfanonin dake sarrafa abincin jarirai ke amfani da wannan lokaci domin tallata abincin jarirai ga mata a kasashen duniya.

WHO da UNICEF sun zayyana wasu hanyoyi da mata za su kiyaye a lokacin da suke shayar da ‘ya’yan su nono domin kare su daga kamuwa da Korona.

Ga hanyoyin

1. Uwa ta wanke hannayenta da ruwa da sabulu ko kuma da sinadarin tsaftace hannu kafin ta dauki da ko ‘yarta.

2. A yi amfani da takunkumin rufe fuska a duk lokacin da za a dauki ko shayar da da ko ‘ya nono.

3. A yi tari ko atishawa a gwiwar hannu ko kuma a yi amfani da tissue.

4. A tsaftace muhalli domin guje wa kamuwa da cututtuka.

5. Uwa za ta iya kiyaye sauran sharuddan gujewa wa kamuwa da cutar koda bata da takunkumin rufe baki da hanci.

Share.

game da Author