Ma’aikatan Sufuri ta jihar Kaduna ta dakatar da masu aikin haya da Keke Napep aiki a babban titin da ya ratsa Kaduna tundaga Kawo har Mahadar Kwamand.
Wannan sanarwa ta fito daga ofis shin ma’aikatar Sufuri na jihar ne wanda shugaban hukumar Aisha Said-Bala ta saka wa hannu.
Sannan kuma hukumar ta ce ƴan dokan jihar, wato KASTELEA za su bazu ta ko-ina a jihar domin tabbatar da masu Keke Napep sun bi wannan umarni da doka.
Bayan haka kuma, hukumar ta umarci masu motocin haya su garzaya hukumar domin sabunta rajistar motocinsu wanda za a fara dada 30 ga Agusta zuwa 30 ga Satumba.
Masu Keke-Napep a jihar sun koka matuka game da wannan sabon doka.
Wani matuki ya ce yanzu ya zama kenan kowa zai yi aiki ne a unguwar sa. Babu ketarawa wani unguwa ba.