Hukumar Sa-ido Kan Hana Laifukan Da Suka Saba Shari’ar Musulunci (Hisbah), ta bayyana kamawa da fasa kwalaben giya 588 a karamar hukumar Ringim dake jihar Jigawa.
Kwamanda hukumar Ibrahim Dahiru ya Sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a garin Dutse.
Dahiru ya ce hukumar ta fasa kwalaben giyan ne ranar 29 ga watan Agusta.
Ya ce sun kwato kwalaban gidan daga kauyukan Tudun Babaye, Gujungu, Kijawal da Wadugur dake karamar hukumar Ringim.
Dahiru ya bayyana cewa addinin Musulunci ya haramta shan jiya da duk sauran wasu abubuwan sa maye da bugarwa a birni da kauyukan jihar.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da Kama Kuma ta hana masu aikata miyagun aiyukka irin haka a al’umma.
Idan ba a manta ba a watan Satumba na shekaran 2019 ne Hukumar Hisbah ta kamawa Kuma ta fasa kwalaben giya 196,400 duk a cikin Kano.
An fasa kwalaben giyan a dajin Kalemawa, cikin Karamar Hukumar Dawakin Tofa, inda Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa addinin Musulunci ya haramta shan jiya da duk sauran wasu abubuwan sa maye da bugarwa, wadanda za su iya yi wa kwakwarwar mutum lahani.
“ Malaman mu na addinin musulunci, da shugabannin mu su hada hannu domin yaki da wannan lamari na kawar da kayan shaye-shaye masu bugarwa.” Inji Ganduje.