Idan ba a manta ba wani daliban jami’ar Kimiyya da Fasaha na Akure mai suna Afolabi Emmanuel yayi wa shafukan yanar gizo shigar-kutse, domin durkusar da shafin PREMIUM TIMES.
Shugaban sashen yada labarai na jami’ar Adegbenro Adebanjo, ya aika wa PREMIUM TIMES takardar sanar mata cewa jma’ar ta dakatar da wannan dalibi daga jami’ar.
” Daga yanzu kada ka kuskura ka kusanci koda katangar jami’ar ne. Jami’ar ta yi tir da wannan kutse da Emmanuel yayi wa shafin PREMIUM TIMES.”
Yadda Jami’ar Fasaha ta Akure (FUTA) ta yi kokarin durkusar da shafin PREMIUM TIMES a intanet
Jami’ar Fasaha ta Akure (FUTA) ta dauki nauyin wani gogarman yi wa shafukan yanar gizo shigar-kutse, domin durkusar da shafin PREMIUM TIMES, fitacciyar jaridar ‘online’ da ke Najeriya.
Wannan gogarman tsallaka shingayen gidajen yanar gizo wato intanet, ya yi duk wata dabarar da masu harkallar kutse a shafukan mutane ke bi su shiga shafukan su, amma bai yi nasara ba.
Ya fara jaraba yin shigar kutsen ne, wato ‘hacking’ tun a ranar 28 Ga Fabrairu, inda ya jibge muggan makaman kayan aikin sa a harabar Jami’ar, kuma ya ya rika kai hare-haren sa ta hanyar yin amfani ‘data’ din jami’ar.
A gefe daya kuma idan ya yi kokarin kutsawa rumbun intanet na PREMIUM TIMES da kwamfuta, sai kuma ya sake kai wani harin da wayar GSM din sa.
Kwanaki biyar cur ya shafe ya na saran kofar shiga shafin Babban Rumbun PREMIUM TIMES, amma bai yi nasara ba, duk kuwa da cewa ya yi amfani da muggan makaman fasahar zamani daban-daban.
Bai samu nasarar kutsawa ba, saboda jami’ar ba ta san cewa jaridar PREMIUM TIMES ta na da kwakkwan shirin da ta ke da shi, wanda ta gina gabjejiyar kuma gadangarkamar kofar da wani dan dagaji bai isa ya fasa ta ba.
Sannan kuma PREMIUM ta da gwarazan jami’an tsaron shafin Babban Rumbun Intanet din ta na zamani da suka hada da Sarkin Yakin PREMIUM TIMES da Babban Dakare, Garkuwar Yanar Gizon PREMIUM TIMES.
Wadannan jami’an tsaron da suke da kwarewar zamani wajen murkushe duk wani gungun mahara ko wani barden da ya nemi yin kumumuwa shi kadai, ko yin shahadar-kudan kokarin afkawa cikin Rumbun Bayanan PREMIUM TIMES.
Irin Makaman Da Dan Shigar-kutsen Intanet Ya Rika Kai Wa Shafin PREMIUM TIMES Hari Da Su:
1. Karfe 8 na safe ya fara sukuwa da zamiya kofar Babban Rumbun PREMIUM TIMES, domin ya ga ta yadda zai yi kunar-bakin-wake ya kutsa a ciki, ya ruguza rumbun gaba daya.
2. Da bai yi nasara ba a cikin dare, washegari kuma da sassafe, karfe 6:15 sai ya sake jaraba sa’a, wannan karon ta hanyar yin amfani da ‘WPScan, abin da ake yi domin a gano karfi ko rashin karfin matakan tsaron shafukan Intanet manya irin na PREMIUM TIMES.
3. Bayan minti 90 ne sai ya fara yunkurin kutsawa da karfin dabarun fasahar zamani na na’ura mai kwakwalwa, wato ‘custom script’.
4. Da safe ne kuma ya yi duk wani kokarin da zai yi ta hanyar siddabarun na’urar kwamfuta domin ya kulle shafin PREMIUM TIMES gaba daya.
Yadda Mai Gona Ya Yi Maganin Mabarnacin Biri:
Wannan mai shigar kutsen bai san cewa PREMIUM TIMES ta yi kwakkwaran tanajin maganin kananan beraye da manyan biran da ke shiga gonakin shafukan sadarwar zamani su na kutsen rufe shafi ko kwace shafin sukutum ba.
Wannan rashin sanin na sa ne ya sa dukkan kayan faman da ya yi amfani da su, gaba daya tsoffin kamaman da ba su iya yi wa PREMIUM TIMES wata illa ko lahani ne.
A wannan rana ya sha wahalar banza ya gaji domin ya bi ta hanyar kai hari da DDOS ne a Rariyar Likau din NTP, wacce tsohuwar hanya ce da aka rika amfani da ita tun Kano na kauye.
Ranar 3 Ga Maris ne ya yi duk wata dabarar da ta rage a kwakwalwa da tunanin sa, amma duk bai yi nasara ba.
Wannan yunkurin karya kofar Babban Rumbun PREMIUM TIMES ya zo ne kwanaki kadan bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin kwatagwangwamar takun-saka tsakanin Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a Fannin Tsaro, Babagana Monguno shi da tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Marigayi Abba Kyari.
Wasu da ke cikin Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure, sun gulmata wa PREMIUM TIMES cewa jami’ar ta dauko sojan-hayar wasu manyan berayen da ke wa shafukan Intanet shigar-kutse, domin su yi wa shafi da Babban Rumbun PREMIUM TIMES dirar-mikiya, su lalata ko su ruguza shi.
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi jami’ar ta FUTA, ta nesanta kan ta da wannan yunkurin na kokarin afkawa Babban Rumbun PREMIUM TIMES na Intanet.
FUTA ta ce sai dai idan wani mai karambani ne kawai da ke dalibta a jami’ar ya yi kokarin shi kadai, ba da yawun FUTA ba.
Discussion about this post