Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar sa ta shirya tsaf domin gudanar da zaben gwamnan Jihar Edo, wanda za a jefa kuri’a a ranar 19 Ga Satumba.
Yakubu ya yi wannan bayani mai karfafa guiwa a ranar Alhamis, lokacin da ya ke ganawa da Kwamitin Tuntubar Harkokin Tsaron Gudanar da Zabe a Benin, babban birnin Jihar Edo.
Farfesa ya ce INEC ya zuwa yanzu ta samu nasarar aiwatar da tsare-tsare har guda 10 daga cikin 14 da suka kudiri aniyar aiwatarwa dangane da zaben.
Yakubu ya kara da cewa, “dalilin wannan ziyara da na kaso shi ne domin ns ga irin shirye-shiryen da aka fara tun yanzu kafin gabatowar ranar zabe. Tabbas mu na samun dukkan rahotannin shirye-shiryen da ke gudana. Amma duk da haka mu ka ga ya dace mu zo da kan mu, domin gani da idon mu karara.
“Wannan hukuma ta fitar da jadawalin tsare-tsaren yadda matakan zabukan Edo da Ondo za su gudana, tun a ranar 6 Ga Fabrairu, 2020. Kenan mun bayar da sararin watanni kusan bakwai zuwa takwas domin a shirya wa zabubbukan biyu sosai.
“To a yau ina farin cikin cewa mun aiwatar da tsare-tsare 10 daga cikin 14 da INEC ta shirya aiwatarwa. Kuma babu wanda aka samu wani tsaikon da har sai da ta kai an sake daga ranar da za a aiwatar da shi.
Abu na karshe shi ne damka rajistar gaba dayan masu jefa kuri’a adadin su baki daya ga jam’iyyu 14 da za su fafata takara ” Inji Yakubu.
Ya ce ayyuka hudu da suka rage wa INEC sun hada buga sanarwar zabe da za a yi ranar Talata mai zuwa, gabatar da sunayen ejan-ejan na kowace jam’iyyar da ta shiga takara, duk a rana daya.
“Sai kuma dakatar da kamfen sa’o’i 24 kafin zabe. Kenan za a dakatar da kamfen 12 na daren Alhamis, kafin Asabar din da za a yi zabe.
“Saboda haka mu dai sai mu ce mun ma rigaya mun kimtsa, sai jiran zuwan ranar zabe kawai.” Inji Yakubu.
Sai dai kuma ya yi tsinkayen cewa zaben gwamnan jihar Edo ne zaben farko da INEC za ta fara gudanarwa a lokacin korona.
A kan haka ya ce hukumar zabe ta fito da ka’idojin yadda za a gudanar da zaben a wannan yanayi da ake ciki.
“Mun jaraba tsarin da ka’idojin a wani karamin zaben cike,-gurbi a Jihar Nasarawa. Kuma mun shirya maimaita tsarin a wannan babban zabe a Edo.”
Tun da farko Kwamishinan Zabe na Jihar Edo, Johnson Alalibo, cewa ya yi akwai masu rajista mutum milyan 2,210,534 a Jihar Edo. Ya ce milyan 1,159,325 maza ne, mata kuma milyan 1,051,209.