Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 31 ga Oktoba ne za a yi zabubbukan cike gurbi na mazabu guda 12 waɗanda su ka rage a dukkan fadin Nijeriya.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa wadda Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, ya bayar a Abuja ranar Talata.
Mista Okoye ya ce in ba domin annobar korona (Covid-19) da ake fama da ita ba, to da tun tuni hukumar ta aiwatar da zabubbukan.
Ya ce: “Tun daga lokacin, hukumar ta fito da sabon tsari domin gudanar da zaɓe a cikin yanayin annobar korona.
“Haka kuma ta sake yi wa ƙa’idoji da dokokin ta kwaskwarima tare da haɗa gwiwa da hukumomin kiwon lafiya da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an yi zabe cikin kare lafiya da tabbatar da adalci.
“Bayan haka, hukumar ta samu nasarar gudanar da zaɓe don cike gurbi a Mazabar Tsakiya ta Jihar Nasarawa, sannan za ta ci gaba ta gudanar da zaɓuɓɓuka na gwamnoni a jihohin Edo da Ogun a ranakun 19 ga Satumba da 10 ga Oktoba.”
Zabubbukan cike gurbin da su ka rage su ne na Yankin Tsakiya na Mazabar Sanata a Jihar Bayelsa; Mazabar Yamma ta Sanata a Bayelsa; Mazaɓun Nganzai da Bayo a Jihar Borno; Mazabar Arewa ta Sanata a Jihar Kuros Riba; da Mazaɓar Obudu a Kuros Riba.
Sauran su ne Mazaɓar Arewa ta Sanata a Jihar Imo; Mazabar Gabas ta Sanata a Jihar Legas; Mazabar Kosofe II a Jihar Legas; Mazabar Kudu ta Sanata a Jihar Filato; Mazaɓar Bakura a Jihar Zamfara, da Mazabar Ibaji a Jihar Kogi.
Okoye ya ce an yanke shawarar hakan ne bayan an gama duba tsare-tsaren da aka yi don gudanar da zabubbukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo da kuma sauran zaɓuɓɓukan cike gurabu.
Kwamishinan ya ƙara da cewa za a yi zabubbukan cike gurabun na majalisun tarayya da na jihohi ne a dalilin aje aiki ko mutuwa na membobin majalisun a jihohin takwas da abin ya shafa.
Ya ce: “Bisa ga daidaitaccen jadawalin lokuta da ke akwai, hukumar za ta bada sanarwar zaɓen a ranar 17 ga Agusta a yayin da kuma jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓuɓɓukan share fagen su don fitar da ‘yan takara a tsakanin ranar 24 ga Agusta da ranar 8 ga Satumba.
“Za a fara mika fom-fom da sauran takardun ‘yan takara a ranar 9 ga Satumba sannan a rufe da ƙarfe 6 na yamma a ranar 13 ga Satumba.”
Okoye ya kara da cewa har an ɗora jadawalin lokutan zaɓen da ayyukan da za a gudanar na zabubbukan cike gurbin a gidan yanar hukumar zaben da kuma kafofin soshiyal midiya.
Ya kara da cewa an kuma ja hankalin hukumar zabe ga samuwar guraben da za a cike a Mazaɓar Isi-Uzo ta Jihar Enugu da Mazabar Bakori a Jihar Katsina.
To amma, a cewar sa, Kakakin majalisar kowacce daga cikin wadannan jihohin bai bayyana wa duniya samuwar wadannan guraben ba tukuna.
Ya roki wadanda abin ya shafa, musamman jam’iyyun siyasa, da su kula da jadawalin lokutan zabubbukan kuma su yi aiki sosai da shi.