INEC ta kaddamar da sabon tsarin gudanarwa

0

Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkokin zabe da su haɗa hannu da hukumar wajen karfafa yin amfani da hanyoyin fasaha da tabbatar da gudanar da zabe mai nagarta.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen wani taro ta hanyar intanet wanda aka gudanar don kaddamar da kundin “Sabon Tsarin Sadarwa na INEC” a ranar Juma’a.

Farfesa Yakubu, wanda a taron ya samu wakilcin Festus Okoye, babban kwamishina kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar, ya ce hukumar ta na sane sosai da cewa tilas ne a musanya tsohon tsarin da ake amfani da shi wajen gudanar da zabe da sabon tsari ta hanyar shigo da hanyoyin fasaha na zamani a hankali a hankali.

Ya ce, “Wannan ne dalilin da ya sa mu ka kafa gidan yana domin rajistar ‘yan takara na jam’iyyu, da gidan yana domin rajistar masu sa ido a zabe, da gidan yana domin rajistar ‘yan jarida.

“Domin tabbatar da aminci da inganci wajen bayyana sakamakon zabe, mun gina gidan yana don duba sakamakon zabe inda hukumar kan saka fom mai suna Form EC8A don jama’a su gani.

“Mu a wannan hukuma za mu ci gaba da ƙara wa kan mu sanin makamar aiki da ake amfani da ita a sassan duniya a harkar yada labarai da sadarwa kan harkokin zabe.

“Za mu ci gaba da ƙara wa kan mu ilimi kan al’amurra da hanyoyin zabe, don haka mu na kira ga kafafen yada labarai da kungiyoyi masu zaman kan su da ma duk wanda abin ya shafa da su hada hannu da hukumar wajen amfani da hanyoyin fasaha da kere-kere na zamani a harkokin zabe.

“Mu na kira ga manyan masu ruwa da tsaki da su hada hannu da hukumar don tabbatar da aminci da inganci a zabe da fidda sakamakon zabe.

“Wannan buri namu na son cimma wadannan ƙudirori shi ne dalilin mu na fito da wannan sabon Tsarin Sadarwar.”

Farfesa Yakubu ya bayyana Tsarin Sadarwa na INEC a matsayin cikakken kundi da aka fito da shi don gudanar da al’amurran gudanarwa na cikin gida da na waje a hukumar.

Ya ce an yi tsarin ne saboda a cire aikin garaje da rashin shiri a wajen gudanar da aikin sadarwa a hukumar.

Shugaban ya yi kira ga dukkan wadanda su ka halarci taron da su yi wa kundin tsarin sadarwar karatun ta-natsu don su fahimci manufa da kuma burin kundin.

Haka kuma ya fada masu cewa su kalli kundin ba kawai don fahimtar aikin tsarin sadarwar INEC ba, har ma don gane dimbin jalubalen da ke akwai.

Ya ce akwai wahalar gudanar da aikin sadarwa a cikin gida da waje a daidai lokacin da kowane mutum da kuma kungiyoyi su ke fuskantar kalubalen rayuwar su a dalilin annobar korona da ta zo wa duniya.

Ya ce: “Ya na da wuya mutane da kungiyoyi da hukumomi su tattara hankalin su kan harkar zabe a lokacin da tsoro da damuwa da ma abin da ya fi haka ya addabe su.

“Da wuya a sa mutane da ƙungiyoyi su tattara hankalin su kan harkokin zabe a daidai lokacin da babu maganar da aka fi yi a duniya kamar ta wannan annoba da hanyoyin magance ta.

“Da wuya a sa mutane su tattara hankalin su kan batun zabe a lokacin da su ke fargabar za su iya rasa aikin su ko ma har sun rasa aikin nasu ko kuma su na zama a cikin sansanin ‘yan gudun hijira.

“Da wuya a sa mutane su tattara hankalin su kan batun zaɓe a daidai lokacin zaman dar-dar.”

Farfesa Yakubu ya ƙara da cewa sanar da mutane wani abu da su ke ganin bai zama dole a gare su ba a lokacin da su ke fuskantar annoba ko wahalhalu abu ne da ke bukatar sabbin dabaru da karfafawa, wanda kuma hakan na buƙatar sabbin tunani da dabaru.

”Saboda haka, tilas ne masana da manajoji kan yaɗa labarai da sadarwa su fito da hanyoyi da dabarun da za su sa mutane su tattara hankalin su kan sakonni masu alaƙa da al’amurran gudanar da zabe.

“Haka kuma ya na da muhimmanci a yada irin wadannan sakonni da labaran ta hanyoyin da mutane za su fahimta a sabon yanayin nesantar juna, zaman dole da karuwar masu kamuwa da cuta a kullum.

“Don haka tilas ne manajojin kafafen yada labarai su riƙa aikin su na sadarwa ta hanyar da mutane za su gani su fahimci zabe a matsayin wani abu da ya dace da rayuwar su.”

Har ila yau, shugaban hukumar ya bayyana cewa an fito da Tsarin Sadarwar ne saboda a bai wa INEC damar gudanar da aikin sadarwa yadda ya kamata.

Farfesa Yakubu ya nemi hadin kan dukkan manyan masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa a INEC, tare da cewa hukumar ta na bukatar fahimta da hadin kan kafofin yada labarai domin ta isar da sakonnin ta ga jama’ar Nijeriya.

Lokacin da ya ke gabatar da sharhi kan kundin sabon Tsarin Sadarwa na hukumar, babban sakataren yada labarai na shugaban hukumar ta INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ya ce kundin mai shafi 55 ya kunshi al’amurra da dama wadanda za su inganta harkar sadarwa ta hukumar.

Oyekanmi ya ce kundin ya nanata cewa a tabbatar “kwararru ko ma’aikatan da aka horas ne kaɗai za a dora kan aikin hulda da ‘yan jarida da wayar da kan masu zaɓe a hukumar” a kowane mataki.

Share.

game da Author