Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za ta dakatar da shirye-shiryen gudanar da zabubbukan gwamnoni da za a yi a jihohin Edo da Ondo idan har abubuwan da ‘yan siyasa ke aikatawa ya jawo tarzoma da karya doka.
Kwamishina na Kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zaɓe a hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a Abuja ran Alhamis bayan an yi taro tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki a zabubbukan inda aka tattauna kan al’amura da dama, ciki har da shirye-shiryen zabubbukan.
Mista Okoye ya ce hukumar ta yi lura cikin damuwa matuƙa da yadda al’amura ke kara rincabewa wajen abubuwan da jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayan su ke aikatawa tare da furta maganganun tada fitina a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zabubbukan.
Ya ce: “Wadannan abubuwan sun haɗa har da lalata kayan kamfen na abokan adawa kamar su allunan talla tare da yaƙar juna ta hanyar rikici da furta muggan kalamai.
“Ya na da muhimmanci jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayan su su sani cewa akwai dokoki da ka’idoji da aka shimfiɗa wadanda wajibi ne a bi su a lokacin yakin neman zabe.
“Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyan ta na tabbatar da an bi doka da oda.
“Saboda haka, lallai ne kada jam’iyyu da ‘yan takara su yi tunanin hukumar ba za ta aiwatar da kudirin ta na tabbatar da an bi dokoki da ka’idoji ba kuma ta hukunta duk wani wanda ya zabi ya karya su.
“A shirye hukumar ta ke ta tabbatar da an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihohin biyu da kuma sauran zabubbukan cike gurbi na Majalisar Tarayya da Majalisun Jihohi.”
Okoye ya ce tilas ne jam’iyyun siyasa su fahimci cewa ana shirin gudanar da zabubbukan gwamnonin Edo da Ondo ne a daidai lokacin da annobar korona ta mamaye duniya kuma hukumar na aiki tuƙuru don tabbatar da cewa an kiyaye dukkan matakan kare kai daga cutar kamar yadda hukumar zaben da hukumomin kiwon lafiya su ka tanadar.
Ya ce a yayin da annobar ta ke ragargazar jama’a, ya zama wajibi kada a ƙara jibga wa mutanen jihohin Edo da Ondo nauyin fitinar tashin hankali a lokacin zabubbukan.
“Tilas ne jam’iyyu su tuna da cewa akwai lokutan da dokokin tsarin mulki da na hukumar zabe su ka shata wa zabubbukan Edo da Ondo kuma barazana ko ainihin aiwatar da tarzoma zai iya rusa wadannan lokutan har su haifar da rikici da ya danganci tsarin mulki.
“Hukumar za ta ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a jihohin biyu a kan bukatar da ke akwai ta gudanar da zabe cikin kwanciyar lumana, musamman ganin cewa ta kashe makudan kuɗin jama’a don shirya zabubbukan.
“Hukumar za ta dauki babban mataki kan duk wani abu da ‘yan siyasa za su yi wanda zai tada hankalin jama’a.”
Okoye ya ce za ta yi aiki tare da haɗa gwiwa da hukumomin tsaro don magance duk wani abu ko wata barazanar tada hankali kafin da kuma lokacin zabubbukan.
“Tilas ne hukumomin da aka ɗora wa alhaki a zabubbukan, musamman waɗanda su ka danganci mahance rashin zaman lafiya da yaɗa maganganun ɓatanci da yin amfani da kafofin yaɗa labarai ta hanyar da ba ta kamata ba, su tashi tsaye a aikin su don tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka kama ya na karya doka.”
Hukumar ta kwantar wa da al’ummomin Edo da Ondo hankali da cewa ta kudiri aniyar yin zabe bisa adalci da lumana a jihohin biyu, sannan ta yi kira a gare su da su mara wa shirin goyon baya.
Discussion about this post