Hukumar Yaki da Sha da Safarar Kwayoyi, NDLEA ta bayyana cewa ta kama tulin kwayoyi kala daban-daban mai nauyin kilo 3,546 a Abuja.
Kwayar wadda kwatankwacin nauyin ta ya kai nauyin garsakeken kato 60, an kama ta ne a unguwanni da garuruwan Abuja daban-daban tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, 2020.
Kwamandan NDLEA na Abuja FCT, Lawan Hamisu, ya ce an kuma kama ‘yan kwaya da masu safarar ta har su 205 a cikin watannin Janairu zuwa Yuli.
Ya ce cikin watannin bakwai ba a yi kame da dama ba, saboda zaman gida da aka yi na killace mutane lokacin cutar Coronavirus.
“Amma a yanzu mun koma farautar ‘yan kwaya da dillalan su, amma a bisa taka-tsantsan da ka’idojin kiyayewar kamuwa da Coronavirus.
“Mun kama tabar wiwi har kilo 3,295.193; kwayar Diazepam kilo 4.975; kilo 2.46 na kwayar Exol; kilo 242.267 na kwayar Tramadol sai kilo 0.842 na Rophynol.”
Hamisu ya ce jimilla sun kama kilo giram 3,546 daidai kenan.
“Babban abin tayar da hankali dai shi ne yadda kwayar koken, wato hodar-Iblis ta zama ruwan-dare a gidaje da dama a Abuja. Gaskiya akwai damuwa kan yawan masu shan kwsyoyi, musamman a tsakanin matasa dakibaii, matan aure da kuma karuwai.
Ya ce an kama maza 180, mata 25 sannan kuma an gurfanar da mutum 75 kotu.
“Wasu mutum 80 kuma an tura su bangaren bada shawara, kuma akwai mutum 10 nuskakku da suka kawo kan su da kan su domin a kula da yadda za su daina shan kwayoyi.”