Hukumar FCT ta rusa gidaje 134 a Abuja

0

Hukumar Babban Birnin Tarayya, FCT ta ruguje gidajen kabilun asalin Abuja har gidaje 134.

Gidajen da aka rushe din suna ‘yankin Apo Akpmajenja ne, da aka ce an rushe domin domin ketawa a shimfida kwalta da za ta bi ta wurin.

Hukumar Kula da Tsaftace Abuja da garuruwan da ke kewayen ta da karkashin Shugaban Kwamiti, Ikharo Attah.

Darakta Muktar Galadima ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa tun watan Janairu aka yi wa gidajen jan fentin da ke nunin cewa a ko da yaushe hukuma za ta iya rushe gidajen.

Galadima ya kara da cewa ko kafin a rushe gidajen, sai da hukuma ta zauna da mutanen da yankin ta sanar tare da shawartar su cewa su tashi daga gidajen na su.

Ya kara da cewa unguwar da suke ta na daga cikin wuraren da gwamnati ta kebe domin gina babban titi a Kudancin Abuja (OSEX). Ya ce matsugunin da kabilun ke zaune za a yi shimfidediyar kwalta ce wadda za ta hade da titin Oladipo Diya, da ke kudancin birnin Abuja.

Daraktan Tsere-tsare da sake tsugunar da wadanda aka tasa daga gidajen su, Nasir Suleiman, ya ce wadanda aka rusa wa gidajen duk an bai wa wasu magudanta 131 wasu gidajen. Sai kuma an bai wa wasu 169 filayen da za su gina wasu gidajen.

Ya ce an samar da filin da za a gina gida da fadar basaraken yankin da kuma wasu filayen da aka yanka domin sayarwa ga jama’a daban.

Baba Lawan, Daraktan Kula da Tsaftace FCT ya ce wadanda aka rushe wa matsugunan tuni sun koma inda aka tanadar musu, kuma unguwar zai zama wurin hada-hadar kasuwanci sosai.

Ya ce kafin a tashe su, matsugunin na fama da kazanta da rashin tsafta, kuma ya na haifar da tsananin cinkoson motoci masu wucewa.

Share.

game da Author