Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, wanda ya yi shugabancin Najeriya sau biyu, ya shawarci matasan Afrika cewa sai sun yi da gaske idan su na so ragamar mulki ta koma hannun su, daga kamun-kazar-kukun da dattawa suka yi wa mulki a Afrika.
Ya nuna damuwa dangane da yadda dattawa suka yi wa mulki kaka-gida, wadanda sau da yawa ke taka gadon bayan matasa su na hayewa kujerun mulki, ta hanyar zame musu ‘yan-amshin-Shatan siyasar su.
Obasanjo wanda ya ci albarkacin dora tsofaffi kan mulki, har ya ci nasa zamanin, ya ce sai matasa sun tashi haikan sun shiga siyasa domin su karbe mulki daga hannun dattawa. Ya ce ihun-ka-banza idan matasa na shiga siyasa amma su na bugewa a matsayin yaran siyasar dattawa.
” Sai fa kun yi wa dattawa irin matsar da ake yi wa gyada a fitar da man kuli-kuli sannan za ku iya karbe ragamar mulki daga hannun su.
” Akwai wasu har su kan wuce shekaru 80, amma sai su rike kujerar mulki, ba su son su sauka matasa su dandana.
“To ni irin wannan canjin na ke so mu maida hankali mu tabbatar mu ga cewa an saka shi cikin kudin dokokin kowace jam’iyya, ta yadda za a bai wa masu karancin shekaru shugabanci, ba tsofaffi ba.
” Misali a ce dokar jam’iyya ta gindaya cewa kashi 50 bisa 100 na mukaman da za a raba idan an ci zabe, zai kasance duk ‘yan kasa da shekaru 40 za a dauka, ko za a nada, ko kuma za a zaba.
Obasanjo ya ce idan aka yi haka, sannan sai a ce ko zabe ma ya kasance kashi 50 bisa 100 na ‘yan takara su kasance ba su wuce shekaru 40 ba.”
Matasan Youth Development Centre, wani reshe na Hukumar Gudanarwar Dakin Karatun Obasanjo suka shirya taron a Oke-Modan, Abeokuta, Jihar Ogun.
An haifi Obasanjo cikin 1937. Shi ne na farkon wanda ya fara yin shugabancin mulkin soja, kuma ya yi na farar hula tsawon wa’adin zango biyu.
Discussion about this post