Harkokin Noma sun kara bunkasa arzikin Najeriya, duk da matsin tattalin arzikin da aka shiga

0

Fannin noma a Najeriya ya kara wa tattalin arziki bunkasa da kashi 24.6 a watannin Afrilu, Mayu zuwa Yuni, fiye da watannin Janairu, Fabrairu da Maris, da kuma watannin Afrilu da Mayu da Yunin shekara ta 2019.

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa ce ta bayyana haka s cikin rahoton da ta fitar a ranar Litinin.

Bayanan da hukumar ta fitar a ranar Litinin, sun nuna cewa Karfin Tattalin Arzikin Cikin Gida na Najeriya ya ragu sosai a watannin Afrilu, Mayu da Yunin 2020.

Karfin Arzikin Cikin Gida (GDP) shi ne karfi da yawan cinikin kayan gida da ake sarrafawa a cikin kasa da kuma ayyukan hada-hadar kudade da aka yi a cikin kasa.

“Fannin noma ya taimaka da kashi 24.65 a watannin Afrilu, Mayu da Yuni na 2030, fiye da na wadannan watanni uku a shekarar 2019, inda aka samu kashi 22.78. Kuma fiye da watannin Janairu, Fabrairu da Maris, na 2020, inda aka samu kashi 22.96.

“Hakan ya nuna a shekara an samu karin kashi 19.90 a wannan zangon watanni uku.”

Wato idan aka auna da kuma yin la’akari da hauhawar farashi da tsadar kayayyaki, za a ga cewa fannin noma ya bada gudummawar kashi 23.9 ga Karfin Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) a Najeriya kenan.

Wato noma ya kara bunkasa karfin tattalin arziki da kashi 1.58 na tattalin arzikin kasa baki daya, daga 2019 zuwa 2020.

Rahoton ya ce shi kankin kan sa fannin noma ya karu da kashi 6.57 idan aka kwatanta bunkasar sa tsakanin watannin Janairu zuwa Maris a farkon shekarar 2020.

Fannin noma a Najeriya ya kunshi fannoni hudu da suka hada da noman kayan abinci, kiwon dabbobi, bunkasa gandun dazuka da kuma kiwon kifi.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Tattalin Arzikin Cikin Gida na Najeriya (GDP) ta kakare tare da yin tafiyar-kura, abin da aka fi sani da ci gaban mai ginin rijiya, a tsakanin watannin Afrilu, Mayu da Yuni na shekarar 2020.

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), mallakar gwamnatin tarayya ce ta bayyana haka a ranar Litinin.

Rahoton Bayanan Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) na watannin Afrilu, Mayu da Yuni (Q2 2020), ya nuna cewa saboda tsayawa cak da harkokin cinikayyar kasa da kasa da zirga-zirgar cikin kasashe a lokacin zaman gida tilas saboda cutar Coronavirus, tsakanin Afrilu zuwa karshen Yuni, tattalin arzikin ya shiga jula-jula.

An dai rufe hada-hadar komai da komai a kasashen duniya saboda barkewar annobar Korona a cikin watannin uku.

Najeriya ta kulle komai da komai, tun daga harkokin gwamnatin tarayya, makarantu, kasuwanci, zirga-zirga, masallatai da coci-coci saboda Coronavirus.

NBS ta lura a ranar Litinin cewa wadancan tsauraran matakan da aka gindaya na hana zirga-zirga ne suka haddasa tattalin arzikin xi gida na Najeriya ya rika yin tukin baya-da-baya.

Wannan jula-jula da tattalin arziki ya shiga, ya kawo karshen bunkasar da ake gani ya dan yi cikin shekaru uku,tun bayan kuncin tattalin arzikin da Najeriya ta shiga cikin 2016.

PREMIUM TIMES ta buga labari a cikin makon da ya gabata cewa sama da mutum milyan 50 a Najeriya ba su day cin yau balle na gobe.

A karshen makon nan kuma jaridar Punch ta buga labarin cewa kashi 61 zuwa 63 bisa 100 na ‘yan Najeriya a sayen abincin yau da gobe ‘yan kudaden da suke samu ke tafiya.

Share.

game da Author