Tsohon Ministan Shari’a Mohammed Adoke, ya maka Ministan Shari’a Abubakar Malami a wata kotu da ke birnin Landan, bisa zargin gabatar da takardun shaida na karya a kan sa, yayin dambarwar shari’ar harkallar kudade ta kamfanin P&ID.
A cikin takardar sammacen karar, wanda PREMIUM TIMES ta ci karo da su, Adoke ya nemi Malami ya janye takardun bayanan shaidar da ya bayar kan Adoke din a shari’ar harkallar P&ID.
Harkallar P&ID ta fito fili a shekarar da ta gabata, yayin da wata Kotun Birtaniya ta yanke wa Najeriya hukuncin diyyar dala bilyan 9.6 ga kamfanin P&ID, saboda karya yarjejeniyar kwangila kafa bututun gas.
Kwatagwangwama ta harde yayin da kotu ta ce ba za ta soke hukuncin biyan diyya da Gwamnatin Najeriya ta nemi kotun ta yi ba, har sai Najeriya ta tabbatar mata cewa dama can kwangilar ta harkalla ce aka shirya, an san ba mai yiwuwa ba ce.
Kwangilar dai an rattaba mata hannu cikin 2010, zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Umaru ‘Yar’Adua, lokacin da ya ke jiyya a asibitin Saudi Arabiya.
Cikin karar da Adoke ya shigar, ya yi Ikirarin cewa abubuwan da Malami ya mika wa kotu a kan sa, duk kage ne da kuma sharri.
Adoke ya roki kotu ta cire wannan shaida ta 4 da Malami ya gabatar wa kotu a ranar 5 Ga Disamba, 2019.
Ya kuma nemi gwamnatin tarayya ta cire bayani na sadara ta 11.4, na 23 da 24.4 da aka shigar a kotu, a ranar 5 Ga Disamba, 2019.
Sai kuma bayanan da Malami ya shigar a ranar 6 Ga Maris, na sadara ta 19.3, na 105.1, na 105.4, na 112, 114.2, na 114 da kuma na 115.58.
Babban lauya Paul Erokoro ne lauyan Adoke, kuma shi ne lauyan James Nolan na kamfanin P&ID.
PREMIUM TIMES ta sha buga rahotannin musamman akan wannan dambawar kwangilar da ba a aiwatar da ko Kashi 1% bisa 100% ba, amma ake neman Najeriya ta biya diyyar dala bilyan 9.6.
Discussion about this post