Shugaban Hukumar Lafiya ta Majalisar Dunkin Duniya (WHO), Tedros Ghebreyesus, ya ce wasu magungunan da aka kirkiro domin gwajin warkar da cutar Coronavirus, har sun kai mataki na uku na gwajin ingancin su da kuma sahihancin aikin su.
Ghebreyesus ya yi wannan sanarwar a taron manema labarai ranar Litinin a Hedikwatar WHO da ke birnin Geneva.
Shugaban na WHO ya ce, ” har yau babu wani magani kaifi-daya a duniya da ke warkar da cutar Coronavirus ko hana ta watsuwa da fantsama.
Ya ce kula da lafiya da tsaftar jiki da ta muhalli da kuma aikin dakile cutar su ne mafi muhimmanci a yanzu.
“A yanzu fadada aikin gwaji da bayar da magani da gano wadanda aka dauki cutar a jikin su, shi ne abin da za a fi maida hankali.”
Sannan kuma ya yi gargadin cewa gaggauta janye dokar hana cakuduwar a cikin al’ummar jama’a zai iya sa Coronavirus ta dawo da karfin gaske.
Ya ce kakkabe Korona da dakile ta, wani kisan-baki ne, sai an yi gayyar taro. Don haka ya ce “idan muka hada hannaye wuri daya, ba mu makara ba, za mu iya fitar da kitse daga wuta. Za su iya ceto rayuwar al’umma da rayukan su. Amma fa sai an hada hannu da karfi wuri daya.”
Ya shaida wa ‘yan jarida cewa Kwamitin Gaggawa na Coronavirus ya yi taro ranar Juma’a cewa abin damuwa ne ganin yadda watanni shida kenan tun da kwamitin ya fara yi Wa jama’a wannan gargadin.
“Saboda makonnin nan mu na ganin wsu kasashen da suka rika murnar rabuwa da cutar, kuma sun dawo su na fama wata sabuwar barkewar cutar Coronavirus din kuma.
“Mu na kuma gani da bibiyar wasu kasashe ko nahiyoyin da cutar ta fi yi wa illa, yanzu sun shawo ta, su na samun nasarar dakile ta.”
Discussion about this post