Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar ware naira bilyan 13 domin fara shirin samar da matakan tsaro a cikin al’umma, wato ‘community policing’.
Wannan wani shiri ne da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shi domin rage yawan matsalolin tsaro a fadin kasar nan.
An sanar da ware kudaden ne yayin taron Kwamitin Majalisar Bunkasa Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) a ranar Alhamis a Abuja.
Taron bisa jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, shi ne na 6 a cikin 2020, ya kuma samu haalrtar gwamnonin jihohi da Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, wasu manyan jami’an gwamnati.
Amma kuma taron na ‘yar halarta daga nesa ne da ake nuno mahalarta daga ofisoshin su a zaune.
An zartas da cewa Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya ya samu wasu gwamnoni biyu domin su gana da Ministar Harkokin Kudade da kuma Sufeto Janar na ‘yan sanda, ta yadda za a tabbatar an yi amfani da kudaden yadda ya dace.
Gwamna Kayode Fayemi wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnoni, shi ne ya yi jawabi a madadin Kwamitin Wanzar da Kafuwar Tsarin Tsaron Unguwanni da Yankuna.
Sauran batutuwan da aka tattauna sun hada da yanayin da ake ciki a kasar nan kan matsalar cutar Coronavirus, batun barazanar ambaliyar ruwa da kuma batun biyan diyya da wadanda aikin titin gwamnatin tarayya ya bi ta cikin gonakai ko filayen su.
NCDC ta gabatar da bayanin cewa ana samun ragowar masu kamuwa da cutar Korona a kasar nan daga kashi 19.7 zuwa kashi 13.7.
Sannan kuma a farkon fara yin gwajin an rika yi wa mutum 500 gwaji a rana daya a fadin kasar nan. Ya ce yanzu kuwa ana yi wa mutum 3,500 a kowace rana a kasar baki daya.