Gwamnati za ta biya alawus din ma’aikatan lafiya dake kula da masu Korona

0

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fara biyan alawus din ma’aikatan lafiyan dake kula da mutanen da suka kamu da cutar covid-19 a kasar nan daga ranar 10 ga watan Agusta.

Ministan kwadago Chris Ngige ya sanar da haka ranar Alhamis a zaman da ya yi da kungiyar likitoci na NARD a Abuja.

Ngige ya ce gwamnati za ta fara biyan alawus din ma’aikatan dake aiki a asibitocin gwamnati shida kafin ta samu sauran kudadden da za ta bukata domin biyan sauran ma’aikata.

Ya Kuma ce gwamnati za ta hada hannu da ma’aikatar kudi domin ware kudadden horar da likitocin kungiyar a cikin kassafin Kudun shekaran 2020.

“Asibitocin koyarwa da asibitin FMC dake kasar nan za su aika da duk sunayen ma’aikatan da suke samun matsaloli wajen karban alawus da albashin su domin a aika wa hukumar IPPIS.

Ngige ya ce gwamnati ta magance matsalar zaftare wa ma’aikata albashin su domin an aika da sunayen su zuwa ma’aikatar kudi.

Ya ce gwamnati ta sassanta matsalolin da kungiyar ke fama da su a asibitin koyarwa dake Port Harcourt UPTH.

“An gudanar da zaben sabon Shugaban kungiyar NARD na asibitin Amma na rikon kwaryan Wanda zai shugabanci kungiyar daga Nan zuwa Disemba 2020 sannan a shekaran 2021 a gudanar da zaben Shugaban kungiyar.

Shugaban kungiyar NARD Aliyu Sokomba ya jinjina kokarina biyan bukatun kungiyar da gwamnati ta Yi Yana Mai cewa har yanzu akwai sauran bukatunsu da gwamnati bata biya ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda NARD ta ajiye aiki a dukkan manyan asibitocin kasar nan, bayan Gwamnatin Tarayya ta kasa biyan albashin su, kudaden alawus-alawus da kuma kasa wadatar da su da kayan kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus

Share.

game da Author