Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 126 daga cikin tsare-tsaren inganta tattalin arzikin kasar nan domin gyara asibitoci a kasar.
Asibitocin da za a gyara sun hada da asibitin FMC, wuraren yin gwaje-gwajen cututtuka, sashen kula da masu bukatan kula cikin gaggawa, sashen da ake kebe masu fama da cututtukan da ba a son sauran mutane su Kamu, da asibitocin koyarwa dake jihohin 36 a kasar nan.
A shekararun baya ne wasu kawararru a fannin kiwon lafiya suka yi kira ga sassan gwamnati kan hada hannu wajen ware isassun kudade domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Kwararrun sun yi wannan kira ne a taron samun madafa kan samar da kiwon lafiya mai nagarta wa mutane cikin sauki kuma da aka yi a Abuja.
A jawabin sa dan takaran kujerar sanata mai wakiltan Kwara ta Arewa a karkashin inuwar jam’iyyar APC Sadiq Umar ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta dauki al’amuran inganta kiwon lafiyar kasar nan da mahimmanci.
Yace rashin yin haka ne ya sa fannin ke fama da matsalolin rashin kudade inda hakan ya sa take yawan dogaro da tallafin da take samun daga kasashen waje.
Umar yace duk da wadannan tallafi da ake samu babu rawar ganin da gwamnatin ta taka a fannin kiwon lafiya inda hakan ya sa suka fara janye tallafin da suke badawa.