Gwamnan Jigawa Mohammed Abubakar, ya dora laifin tsadar kayan abinci a kan gwamnatin da ta gabata.
Ya ce an rika tafiyar da mulki a makance, wajen maida hankali ga shigo da kayan abinci iri daban-daban a kasar nan, ba tare da yin la’akari a noma irin sa ko madadin sa a kasar nan ba.
Ya yi wannan bayani ne a wurin taron kaddamar da wasu ayyuka na Shiyyoyin Najeriya shida da Ministan Sadarwa Isa Pantami ya yi s Abuja.
“Ta yaya kuwa kayan abinci ba za su yi tsada ba, tunda mun gaji gwamnatin da a lokacin ta ana saida gangar danyen mai dala 100 har zuwa 120, amma ta kasa kirkiro hanyoyin noma abincin da za a ci kasar nan kuma ta hana shigo da shi daga waje?
“Gwamnatin da ta gabata ba ta tanadi wani nagartaccen tsarin wadatar da abinci ko hana shigo da kayayyaki daga waje ba. Sai ya kasance yayin da ake samun makudan kudade, a gefe daya kuma an rika narkar da kudaden wajen shigo da kayayyaki daga kasashen waje, ciki kuwa har da kayan abinci mai dimbin yawan gaske.’ Inji shi.
Gwamnan ya ce kada a ga laifin Buhari wajen faduwar farashin danyen mai da kuma karancin dala a kasuwa. Ya ce hakan duk sun faru ne, saboda gwamnatin baya ta dogara kacokan wajen shigo da kaya daga waje.
“Babu ruwan Buhari da karancin dala. Dala ta ce na karanci ne saboda sai an shigo da ita daga waje. Ana shigo da ita ta hanyar danyen man fetur da ake sayarwa. To yanzu kuma danyen man fetur ya samu cikas, farashin sa ya karye a kasuwa.” Inji gwamnan.
Ya ce dalili kenan har yanzu Najeriya ke shigo da kayayyakin bukatu, ayyuka da gudanarwar bukatu na dole.
A yau ne aka cika cika shekara daya daidai a Shugaba Muhammadu Buhari ya kulle kan iyakokin kasa, aka hana shigo da kayan abinci, musamman shinkafa.
Sai dai jama’a na ta korafin cewa rufe Kan iyakokin ya kara haifar da tsadar kayan abinci da kayan masarufi a cikin kasa.
Discussion about this post