Gwamnan Jihar Bala Mohammed ya nada Balaraba Ibrahim maitaimaka masa kan harkokin ‘yan mata da basu yi aure ba da zawarawa.
Jaridar Punch ta wallafa wannan labari a shafinta ta yanar gizo. Baya ga ita wasu jaridu da dama sun wallafa wannan nadi da gwamna Bala yayi wa Balaraba Ibrahim.
Kamar yadda jaridar ta wallafa, Balaraba tata gode wa gwamnan bisa wannan nadi da yayi mata.
Balaraba Ibrahim ce shugabar kungiyar zawara na jihar Bauchi.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta wallafa wani hira da tayi da Balaraba n da ta shaida mata cewa ta kafa cibiya da zai rika ba mata shawarwari game da yadda za su yi zaman aure.
” Mun gudanar da bincike akan dalilin da ya sa ake samun mace-macen aure a jihar Bauchi a kwanakin baya. Mun yi wannan aiki ne a kananan hukumomi 22 da ke jihar.
” Abin da muka gano shine a mafi yawan lokutta aure kan mutu ne a dalilin tsananin talauci, rashin iya tafiyar da gida ga mazajen mata, rashin sana’a da dai sauran su.
Balaraba ta kara da cewa duk da karancin mazan aure da mata ake fama da shi, wadanda suka yi auren basu iya rike matan na su.
” Akwai mata da dama da suka yi aure tun suna ‘Yan shekaru 15, kafin su kai 20 an sako su saboda rashin jituwa da mazajen su.