Sanata Uba Sani dake wakiltar Kaduna ta tsakiya ya gargadi mutane musamman wadanda ba mazauna Kaduna bane da su rika sara suna duban bakin gatari kan abin da suke fadi game da rikicin Kudancin Kaduna.
” Wannan rikici ce da ta shekara 40 ana fadi-tashi da ita a Kaduna. Ba abu ne wanda wai yanzu ne aka fada cikin sa ba. Kuma gwamna El-Rufai ya na iya kokarin sa wajen ganin an kawo karshen rashin zaman lafiya da ya addabi mazauna yankuna da dama a fadin jihar.
” A shiyya ta, Kaduna ta tsakiya, akwai kananan hukumomin dake fama da hare-haren ‘yan ta’adda da mahara, kamar Igabi, Kajuru, Giwa da sauran su. Wannan matsalar tsaro ba a yankin kudancin Kaduna bane kawai ake fama da ita.
Sanata Uba ya ce a makon da ya gabata rundunar Sojin sama suka kara yawan jami’an su a yankuna dabam dabam a Kaduna domin kawo karshen hare-haren mahara da suka addabi jihar.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, Samson Ayokunle da tawagar manyan limamen kiristoci sun ziyarci gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a fadar gwamnati.
Bababn makasudin zuwan su Kaduna shine don su tattauna da gwamnan kan yadda za a kawo karshen rashin zaman lafiya da ya addabi mutanen jihar musamman yankin Kudancin Kaduna.
A jawabin sa, gwamna El-Rufai ya ce gwamnatin sa ta yi matukar maida hankali wajen ganin an kawo karshen wannan hare-hare.