Guguwar gagarimin tashin farashin man fetur ta tirnike Najeriya

0

Sabon farashin litar man fetur da aka amince a rika amfani da ita, tuni ta fara aiki, inda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kara farashin da kashi 18 bisa 100 na yadda ake sayen fetur din kafin a yi karin.

Yayin da ya tashi daga naira 140.80 zuwa 143 80 a hannun gwamnati, tuni dillalai da masu gidajen sayar da mai sun maida lita daya har naira 150.

Wannan karin farashi, shi ne Hukumar Kayyade Farashin Fetur ta Kasa ta amince a sayar da lita daya a cikin watan Agusta.

Gwamnatin Tarayya ta shigo da wannan sabon tsarin kayyade farashin man fetur a kowane wata, inda ta ce a wani watan farashin ka iya sauka, wani watan kuma zai iya hawa sama, kamar yadda ya hau a yanzu.

Kwamiti ne ke zaunawa a karkashin Hukumar Kayyai Farashin Man Fetur ta Kasa, shi ke zama kowane karshen wata ya yanka farashin da ya ke ganin za a sayi litar man fetur daya a Najeriya.

Ganin an kai sati daya ba a fito da sabon farashi ba, PPMC ta fito da sabon farashi inda ta kara naira 24.84 a kowace litar fetur daya.

Hukumar PPMC wadda ke karkashin NNPC ke da alhakin sayar da fetur din da ake sayarwa a cikin Najeriya.

Saboda haka, duk wani fetur da ake sayarwa a cikin Najeriya, to PPMC ce ke kula da sayar da shi.

Farashin ya karu da naira 24.84 bisa ga yadda aka sayar da shi a watan Yuli. Hakan kuwa ya jawo kakkausan suka ga gwamnatin Buhari.

Karin na faruwa ne saboda kudin lodin mai da saukalen sa da ake sake biya idan aka dauko shi daga daffo-daffo na gwamnatin tarayya.

PREMIUM TIMES ta gano cewa an yi jinkirin bayyana sabon farashin mai a wannan wata na Agusta, saboda gaggauta kwashe ma’aikatan Ofishin Hukumar PPPRA da aka yi, aka umarce su cewa ya rika gudanar da aikin sa daga gida.

PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin yada labarai na ofishin, mai suna Kimchi Apollo, amma bai amsa ba.

An tura masa sakon tes, shi ma bai dauka ba.

Share.

game da Author