Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi kira ga Hukumar Sauraren Kararrakin Cin Hanci Da Rashawa ta jihar cewa kada ta nuna ragowa ko saurara wa duk wani jami’in gwamnati da ya wawuri dukiyar jama’a a gwamnatin sa.
Haka Ganduje ya bayyana a lokacin da ya kai ziyara a ofishin hukumar, a ranar Asabar.
Ya ce gwamnatin tarayya ita kadai ba za ta iya yakar cin rashawa ba, shi ya sa Jihar Kano ta kafa hukuma irin aikin da EFCC ke yi, domin dakile rashawa a gwamnatin Kano da kuma dukkan kananan hukumomin jihar 44.
“Duk wani wanda ya fada cikin komar wannan hukuma, to a tabbatar da ya dandana kudar laifin da ya yi. Duk wanda ku ka damke ba zan yi magana ba, kuma ba zan yi wa hukumar nan katsalandan a aikin ta ba.
“Irin yadda matsalar wawurar kudaden gwamnati ta yi muni a yanzu, to ganin cewa yaki da rashawa na sahun gaba na ajandar gwamnatin Buhari, shi ya sa mu ke wannan kokari, domin cewa gwamnatin tarayya ita kadai ba za ta iya yaki da cin hanci da rashawa ba.
“Sai an fadada yakin zuwa fadin jihohin kasar nan da dukkan kananan hukumomin da ke Najeriya kakaf.” Inji Ganduje
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji, ya ce ya jinjina wa Ganduje saboda jajircewar da ya ce gwamnan na yi wajen yaki da masu wawurar kudaden gwamnati.
Kwanan nan hukumar ta kwato naira 310,000 daga hannun Mashawarcin Gwamna Ganduje a kan Lamurran Addinin Musulunci, mai suna Ali Baba.
An ba shi kudade ne domin ya raba wa limaman da suka taru a gidan gwamnatin Kano, suka yi addu’ar bukatar Allah ya raba Kano da cutar Coronavirus.
Sai dai kuma Ali Baba ya zaftare kudaden, inda ya raba wa kowane limami naira 5,000, maimakon naira 50, 000 kowane da aka ce a biya shi ladar addu’o’in da ya yi.
Jama’a a Kano da Arewacin kassr nan sun rika caccakar hukumar, ganin cewa ba ta gurfanar da Ali Baba gaban shari’a ba.
An rika danganta hukumar da cewa makamin da Ganduje ke amfani da shi ne ya na dakile masu adawa da shi kawai.
Cikin 2018 an kama Ganduje a wasu faya-fayen bidiyo ya na cuc-cusa milyoyin daloli aljihu.
Sai dai kuma saboda ya na gwamna mai dokar kariyar tuhuma, ba a gurfanar da shi kotu ba, kuma wannan abin kwatagwalci da ya yi, bai hana jam’iyyar APC ta sake ba shi takara a zaben 2019 ba.
Discussion about this post