FYADE: Kotu ta yanke wa wani tsoho mai shekaru 60 hukuncin kisa a Kano

0

Kotu a jihar Kano ta yanke wa wani dattatijo mai shekaru 60 hukuncin kisa bayan kama shi da laifin yi wa ‘yar shekara 12 fyade.

Lauyan da ta shigar da karar Badariya Muhammad ya bayyana cewa Mati Abdu ya yi wa yarinyar fyade a karkashin inuwar wata bishiya a kauyen Farsa dake karamar hukumar Tsanyawa a 2019.

Sai da kotun ta yi zama har sau Malam Abdu ya na amsa laifin sa na yun lalata da yar shekara 12.

Alkalin kotun Ibrahim Sarki-Yola ba Abdu kwanaki 30 daga yau ko zai daukaka kara.

Idan ba a manta ba a watan Yuli ne gwamnatin Kano ta bada shelar cewa duk wani mai tsohon kangon gina a jihar ya gine shi ko kuma a daure shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna ya bayyana haka ranar Alhamis ganin yawan fyade da ake yi wa kananan ‘yan mata a Kano, yana faruwa ne a tsohon kangon ginin da ba a gama gina shi ba,

Haruna ya ce a dalilin haka jami’an tsaro za su rika bin duk wani kagon gini dake jihar suna cafke wadanda ke boyewa ciki suna tafka barna.

” Duk wanda aka kama da laifin aikata wani mummunar abu a irin wani kangon gini, toh laifin zai shafi harda mai mallakin wannan gini.

Haruna ya yi kira masu irin wadannan gine-gine a jihar da su gaggauta gine su tun da wuri.

Sakamakon bincike

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa a tsakanin watannin Janairu zuwa Mayu 2020 an yi wa mata 42 fyade kuma duk suna gaban kuliya.

Sannan kuma akalla kashi 33.3 bisa 100 na aukuwa ne a ire-iren wadannan kangon gini da ba a kammala su ba.

Kashi 17.7 a gonaki, 15.6 a shaguna, 15.6 a dakuna sannan kashi 8.9 a makarantun kashi 2.2 kuma a kasuwani.

A karshe rundunar ta gargadi masu aikata irin wadannan laifuka su shiga taitayin su domin hukumar ba za ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda aka kama da laifin aikata hakan.

Share.

game da Author