Duk bashin da Najeriya ke ciwowa mai dalili ne -Lai Mohammed

0

Dukkan basussukan da Najeriya ke ciwowa masu dalili ne, domin su na da muhimmanci sosai, saboda ana gina ayyukan ci gaban kasa da inganta rayuwar jama’a da su ne.

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a tashar jirgin kasa ta Obafemi Awolowo da aka gina kan sabuwar hanyar jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan.

Minista Lai shi da Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ne suka Kai ziyarar dubagarin sabon titin mai tsawon kilomita 156 daga Lagos zuwa Ibadan.

Ministocin na tare ne da manyan jami’an hukumar jiragen kasa da kuma jami’an amfanin CCECC, na kasar Chana, wanda shi ne ya yi kwangilar gina titin jirgin kasa da kuma ‘yan jarida.

“Babu wata babbar hanyar da ya kamata mu nuna wa masu korafin bashin da muke ciwowa, kamar mu nuna musu wannan titin jirgin da kuma sauran wasu, domin su ga sun irin abin da muke yi da kudaden da muke ramtowa.

“Babu wani aibi don ana ciwo tulin basussukan da ake yin ayyukan raya kasa da su, matsawar dai ana yin ayyukan.

“Babu aibu don ana ciwo bashin da ake ayyukan raya kasa da su ana samar da dimbin ayyukan yi kuma ana bunkasa tattalin arzikin kasa.”

Lai ya kuma yaba wa Minista Amaechi tare da yi masa jinjina kan namijin kokarin da ya yi, tare da nuna gamsuwa da nagartar aikin titin jirgin kasa din.

Minista Amaechi ya ce kudi ba za su zama matsala ba wajen kammala aikin titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan, domin yanzu haka akwai tsabar kudi ajiye har daka bilyan 1.6 gsngariya.

Share.

game da Author