Don Allah Wace Doka Ce Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II Ya Karya? Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

‘Yan uwa masoya, masu daraja, masu albarka. Kamar yadda kuka sani, dimbin masoya daban-daban, da mutanen arziki kala-kala, da abokan hulda daga ko wane sako da lungu na kasar nan, da ma duniya baki daya, suna ta yin tururuwa zuwa Birnin Lagos domin yin gaisuwa ga Malam Muhammadu Sanusi II. Da yake shi, kamar yadda kowa ya san shi, kuma duniya ta shaida, mutum ne mai nuna tausayi da jin kai ga mutane baki daya da musamman talakawa. To shine yasa ya yanke shawarar kai ziyara Birnin Kaduna, garin Gwamna, domin yayi sati daya can, da nufin saukakawa duk masu son zuwa gaishe shi. Wato kenan, maimakon su tafi Lagos, to yanzu ga shi a Kaduna domin abun yazo masu da sauki.

Kuma wannan ziyara, kamar yadda kowa ya sani ne, dole mutane za su ta yi mata fassara iri-iri, daban-daban. Wasu zasu yi kokarin dangatata ga maganar siyasa, wasu kuma wani abun na daban. To amma koma dai menene, ba yadda zaka iya hana mutane fadar ra’ayinsu. Amma dai abu ne sananne, wallahi wannan ziyara sam babu maganar siyasa a cikinta. Domin dai Malam Muhammadu Sanusi II ba dan siyasa ba ne, kuma ba zai yi siyasa ba.

Yin wannan ziyara ke da wuya, kawai sai makiya suka fara aikin na su na hassada da sharri da nunkufurci. Suna ta maganganun banza da wofi, na bata lokaci. Da yake su aiki bai ishe su ba.

Ya ku jama’ah, idan kun lura, wasu mutane, hassada kawai ce da bakin ciki yasa ba su son Malam Muhammadu Sanusi II. Wasu kuma suna ganin ya tare masu wata hanyar cin abinci, domin yana fallasa hanyoyinsu marasa kyawo, talakawa kuma suna fahimta, suna ganewa. Kuma su har kullun, sun fi son a bar talaka a duhu, kar a bari su san me ke faruwa. Shi kuwa Malam Muhammadu Sanusi II yace a’a.

A da can sunce ya cika surutu. Amma duk da yanzu yayi shiru, ba ya magana, basu kyale shi ba.

Sun ce yana goyon bayan yahudawa, don haka bai cancanci ya shugabanci al’ummar Hausa-Fulani ba. To yanzu ba ya kan sarautar, amma duk da haka basu kyale shi ba. To kenan me wadannan mutane suke so ne kuma meye manufarsu?

Kawai bakin cikin su shine, me yasa Malam Muhammadu Sanusi II zai sa babbar riga da alkyabba, kuma ya rika sanda. Kuma sun kasa kawo wata dokar da ta hana yin hakan. Domin mu bamu san wata dokar da ta hana yin hakan ba!

Yanzu kuma da ace ‘yar T-shirt ko shirt ya koma yana sawa, to da sai su fara murna, suna yadawa, suna cewa dama mun fada maku bayahude ne, kalli irin kayan da yake sa wa.

Sannan kuma wai suna bakin cikin me yasa za’a yi masa algaita. Ikon Allah, jahilan banza. To yau algaita ko wanda ba dan sarauta ba, ai idan yana so, za’a iya yi masa ta kudin sa, bare kuma Sarki, dan sarauta, jinin sarauta, irin Malam Muhammadu Sanusi II.

Kuma wai suna bakin ciki me yasa zai hau babbar mota. Kai jama’ah, wai wadannan mutane burin su shine, su gan shi tsaye yana ciniki da mai Keke Napep a gefen hanya, shi kenan hankalin su ya kwanta ko? To ta Allah ba taku ba!

Wai kuma suna bakin cikin su ga mutane suna nuna masa soyyaya. Wai burin su, su gan shi shi kadai, ba kowa, ko kuma su ga ana jifar sa, ana yi masa ihu. Shi kuma Allah sai yaki hakan, sai ya tara masa dimbin masoya, masu son sa so na gaskiya, ba irin son da ake yi masu su ‘yan siyasa ba.

Duk fatan ku na sharri zuwa ga Malam Muhammadu Sanusi II da ikon Allah ba zai tabbata ba. Da yardar Allah Malam Muhammadu Sanusi II ba zai tsiyace ba duniya da lahira.

Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II har gobe ruwa na maganin dauda. Allah ya tara masa jama’ah. Kuma kullun farin jininsa sai dada karuwa yake yi. Duk wannan ba domin komai ba, sai don ya rike Allah, kuma ba ya nufin kowa da sharri.

Makiya kullun sabbin makirce-makirce suke ta fitowa da su, amma Allah ya kare bawansa, Allah ya kare abun sa, saboda farar aniyarsa ga ko wane mutum. Sun kasa yin komai, sun hakura, sun dukawa izza da kwarjinin wannan bawan Allah.

Jiya lahadi, 23/08/2020, fadar Kano babu kowa, tayi tsit, tayi shiru, duk sun watse, sun tafi tarbon Malam Muhammadu Sanusi II a Birnin Kaduna garin Gwamna, garin Malam Nasiru El-Rufa’i maganin shedanu da tsageru. Sannan yanzu haka daruruwan mutane daga jihohi daban-daban, suna nan kan hanyar su ta zuwa birnin Kaduna garin Gwamna, domin kai caffarsu da gaisuwar ban girma ga wannan bawan Allah, mai farar aniya.

To duk wannan ne fa yasa wadannan mutane, masu rayuwar nunkufurci, wadanda basu iya yin tasu rayuwa ba tare da sun sa ido ga rayuwar wani ba, suka sake bude wasu sabbin shafuka a soshiyal midiya, domin sukar wannan ziyara mai albarka da aka yi da kyakkyawar niyyah. Ita dai hassada, kowa ya sani, ga mai rabo taki ce!

Ina rokon Allah ya kara rushe makiyan jihar Kano, makiya al’ummar Kano da arewacin Nigeria, da makiya zaman lafiyar Kano, arewa da Nigeria baki daya, amin.

Kai jama’ah, wai har na ga jahilan suna yada cewa za’a yi bincike a masarautar Kano, duk wadanda suka tafi tarbon Malam Muhammadu Sanusi II a Kaduna za’a dauki mataki a kan su. To idan har zasu dauki mataki, sai dai a dauka akan kowa da kowa. Domin dai fadar Kano babu kowa, duk an dade a Kaduna wurin Malam Muhammadu Sanusi II. Wadanda ma basu samu damar zuwa ba, mun san uzuri ne ya hana su, amma da ikon Allah, muna sane da cewa suna tare da Khalifah Muhammadu Sanusi II. An baro su wane can cikin zullumi da tagumi.

Wallahi kadan ma kenan, domin mun fada maku cewa duk jihar da Malam Muhammadu Sanusi II ya ziyarta a kasar nan, haka za’a tarbe shi.

Sannan don Allah muna ba wa ‘yan uwa hakuri wadanda suka ce sun samu sanarwar zuwan Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II Kaduna ne a latti. Amma In Shaa Allahu nan gaba, duk jihar da Malam Muhammadu Sanusi II zai ziyarta za’a sanar da wuri.

Sannan daga karshe, ‘yan uwa mu ci gaba da rokon Allah ya taimaki Malam Muhammadu Sanusi II. Kar muyi kasa a gwiwa wurin addu’a. Muyi ta rokon Allah ya ci gaba da daukaka shi da kare shi, ya karya makiyansa, marasa daraja. Domin mun gano cewa basu tsoron Allah, mun gano cewa sun manta da Allah, sun manta da cewa Malam Muhammadu Sanusi II ikon Allah ne, domin wallahi ko baya kan gadon sarauta, to darajar, da martabar, da mutuncin, da girman, da muhibbar, da daukakar duk sunanan, ba in da suka tafi. Kuma ma kadan kenan, domin Allah ne kadai yasan me zai yi wa Malam Muhammadu nan gaba.

Wani yana nan yana ta yawon neman goyon bayan mutane, da bara, da maula, da tumasanci, yana zaton cewa ko zai samu daraja da goyon bayan mutane, amma ina, Allah ya hana masa darajar, kuma ya hana jama’ar! A wata jihar har kudin talakawan jihar aka diba aka saya masa motoci, amma duk bamu ce komai ba, sai yanzu don Malam Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara Kaduna, wannan ne zai zama abun surutu a wurin ku? Haba jama’ah, wai me ya makantar da wadannan mutane ne da basa iya ganin gaskiya su fahimce ta?

Da yardar Allah, nan gaba Allah zai yi wa Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II wani irin girman da ba mu tsammani, domin shi ba abun wasa bane, irin sa mutum ne da ake nema a duniya.

Jahilan banza kawai, idonsu ya makance, sun manta da Allah. Saboda abun da suka so bai kasance ba, burin su bai cika ba. Saboda an fada masu cewa idan aka cire Malam Muhammadu Sanusi II, Awe za’a kai shi ko Loko, shike nan, za’a daina jin labarin sa, a daina ganin sa, a manta da shi. Sun manta cewa, sunyi sake, dan zaki ya girma, kuma ta Allah ba tasu ba.

Gaba dai, Gaba dai, Dan Lamido mai Allah. Wallahi Allah zai ci gaba da dora ka kan makiya, ko wadanne iri ne!

Al’ummar jihar Kaduna, da dukkanin masoya a duk inda suke muna yi maku godiya kwarai, Allah ya bar zumunci, amin.

Wassalamu Alaikum

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author