DILLALIN MUTUWA: Yadda wani tantagaryar dan duniya ya rika karkatar da kasafin kudin Jamhuriyar Nijar, ya na jido makamai daga Rasha

0

Yayin da kungiyoyin ‘yan ta’adda daban-daban ke buwayar Yankin Sahel da munanan hare-hare, wani tantirin dan ta-kife a Jamhuriyar Nijar ya shafe shekaru goma cur ya na karkatar da makudan kudaden Jamhuriyar Nijar, wajen sayo muggan makamai daga Rasha.

Sai dai kuma an gano cewa akwai da hadin-baki da Amurka dan takifen mai suna Abubakar Hima ya rika aiwatar da wannan harkalla da masu bincike suka kiyasta ta kai dala bilyan 1, tsakanin 2011 zuwa 2019.

1. Wata Kungiyar Binciken Kwakwaf ce ta fara fallasa wannan harkalla da ce kashi 1/3 na kudaden cinikin makaman an nunnunka adadin da ya kamata a biya kwangilar.

2. Kungiyar Binciken Kwakwaf mai zaman kanta ta Inspection Generale des Armees ce ta binciki yadda aka rika kashe kasafin kudaden, wanda ta tabbatar da haka.

3. Binciken ya tabbatar da cewa kudin dalar Amurka 320 ne daga cikin dala milyan 875 aka yi wala-walar su da sunan kudaden cinikin makaman sojoji.

4. Da goyon bayan Amurka aka rika wannan harkar hada-hadar makamai, domin cikin shekaru 10 sai da Amurka ta tallafa wa Jamhuriyar Nijar da kudin makamai har dala milyan 240.

5. Kungiyar Binciken Harkallar Cinikin Makamai ta ce an kirkiro cinikin makaman ne hususan domin a karkatar da kudi ne kawai.

6. Bincike ya nuna cewa kudin da aka karkatar za su kai sepa bilyan 76, kwatankwacin dalar Amurka milyan 137.

7. An rika amfani da kamfanonin Rasha, Ukraine da na Chana ana karkatar da kudaden.

8. An rika nunka wa wani kamfanin Amurka kudaden kwangilar ana rubanya adadin da ya kamata a biya ta.

9. An rika bada kwangilar ba tare da buga tandar neman farashi daban-daban daga wasu ‘yan kwangiloli ba

10. Wani masanin sirrin cinikin makamai a asirce, mai suna Andrew Feihstein, ya tababtar da munin wannan harkalla.

11. Gwamnatin Jamhuriyar Nijar na binciken wannan harkallar makamai, wadanda ya sa hankulan wasu manyan cikin gwamnatin kasar ya tashi sosai.

12. Manyan ‘Yan Harkallar Jamhuriyar Nijar: Tantiri Abubakar Hima Da Gogarma Abubakar Charfo

Abubakar Hima ba dan kowa ba ne a Jamhuriyar Nijar. Sai dai mahaifin sa ma’aikacin gwamnatin tarayya ne, a Ma’aikatar Harkokin Noma.

Cikin 2005 ya auri ‘yar Shugaba Ibrahim Bare Mainasara, wanda aka bindige a juyin mulkin 1999.

Shi kuma Abubakar Charfo dan kwangilar gine-gine ne. Ba shi da masaniyar harkokin tsaro, amma ya zama babban gogarman kwangilar sayen makamai da harkalla.

13. Nijar na daga sahun gaba na matalautan kasashe na duniya, amma cikin shekaru 10 din nan ta shiga tsamo-tsamo cikin harkar makamai a duniya, saboda zumuncin da ta kulla da Amurka.

14. Amurka ta kashe dala milyan 280 ta gina sansanin jiragen sama a Agadez, domin yaki da ta’addanci a yankin kasashen Magrib.

15. Amurka na taimakawa Nijar da horas da sojoji da kuma yin atisaye tare. Domin ta na horas da sojojin Nijar kan dabarun yaki da ta’addanci.

Share.

game da Author