Mambobin Majalisar Tarayya na PDP, sun ki yarda da guraben leburori 30 da aka ce za a bai wa kowanen su, domin ya kawo a dauka aikin leburanci a cikin lebura 774,000 da Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a dauka aiki.
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai ta Tarayya, Ndudi Elumelu, ya ce ba su gurabe 30 kacal a cikin leburori 1,000 da za a dauka a kowace Karamar Hukuma wadda dan majalisa ke wakilta, tantagaryar rashin adalci ne. Kuma ba za su yarda da hakan ba.
Elumelu ya ce haka bai yi kama da abin da ake kira adalci ba, ko kadan. Kuma ya ce ba haka ake nuna wakilcin da suke yi wa jama’a ba.
Kowane Dan Majalisar Tarayya dai na wakiltar akalla Karamar Hukuma daya. Akwai masu wakiltar biyu, ko masu uku. Har ma akwai masu wakiltar Kananan Hukumomi hudu. Hakan kuwa ya danganta da yawan girman karamar hukuma ko kuma yawan al’umma da ke cikin kasamar hukumar.
Daukacin Marasa Rinjayen dai a karakshin Elumelu, sun nemi a sake rabo na adalci Kuma sahihi, bayan an sake sabon tsarin da aka bi aka raba guraben yadda ba za a kafci adadin gurabe masu dimbin yawa a bai wa wasu tsirarun ‘yan ba-ni-na-iya a cikin jam’iyyar APC mai rike da mulki ba.”
An dai tsara cewa leburorin da za a dauka, za su fara aiki ne a cikin watan Oktoba. Shirin ya hada rikici tsakanin ‘Yan Majalisa da Ma’aikatar Harkokin Kwadago ta Kasa.
Karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo, wanda Shugaba Buhari ya damka kula da aikin a karkashin sa, ya zargi ‘yan majalisa da kokarin kwace akalar tafiyar da aikin daga hannun sa, duk kuwa cewa an nemi su kawo sunayen kashi 15 bisa 100 na adadin leburorin da za a dauka, su 774,000.
Majalisa ta ce bai kamata a damka tafiyar da aikin a hannun dan siyasa, kuma Ministan Kwadago ba. Inji su, Hukumar Samar Wa Matasa Aiki ta Kasa (NDE) ce ta cancanta ta aiwatar da shirin.
Duk da ‘yan majalisa sun nemi a dakatar da daukar leburorin, gwamnatin Buhari ta yi watsi da kiraye-kiraye da korafe-korafen na su.
Elumelu ya ce ci gaba da daukar leburorin da ake kan yi zai zame masu alakakai, domin su ne kallo a mazabun su a matsayin tudun-dafawa.
“A matsayin mu na wakilai, mu jama’ar karkara suka fi kusanci da su, ba tare da bambancin kabila ko yare ko addini ba.
“Abin tambayar ma ita ce, shin wane ma’auni aka yi amfani da shi aka ba kowane Dan majalisar tarayya gurabe 30 daga cikin mutum 1000. Ina sauran mutum 970 din?
Sai dai Keyamo ya rashin yardar su aikin banza ce, domin dai sauran wadanda za a dauka din dai su 970, ai a cikin Karamar Hukumar da Dan Majalisar ne ke wakilta, ba daga wani wuri za a dauko su ba.
Discussion about this post