Majalisar dokokin jihar Kaduna ta dakatar da wasu mambobin ta guda uku na tsawon watanni 9.
Majalisar ta Kuma kwabbi wasu mambobin majalisar guda biyar sannan ta umurce su da su rubuta wasikar tuba ga majalisar sannan su buga wasikar tuban a jaridun kasar nan na tsawon mako daya.
Majalisar ta yanke wannan hukunci ne a zaman ta na ranar Talata bayan ta saurari rahotan binciken kwamitin da aka nada kan damben da aka taka tsakanin mambobin majalisar a zauren ta ranar 11 ga Yunin 2020.
Mataimakin Kakakin majalisar Isaac Auta-Zankai ya jagoranci zaman da aka yi ranar Talata.
Shugaban kwamitin Shehu Yunusa ya shawarci majalisar da ta dakatar Kuma ta ja kunnen mambobin da suke da hannu a tada rikicin bisa ga dokokin majalisar.
Wadanda aka dakatar sun hada da Mukhtar Isa-Hazob tsohon mataimakin shugaban majalisar dake wakiltan Basawa, Nuhu Goroh-Shadalafiya dake wakiltan Kagarko da Yusuf Liman-Dahiru, Mai wakiltan Kakuri/Makera.
Majalisar ta ja kunnen Salisu Isa dake wakiltan Magajin Gari, tsohon kakakin majalisa dake wakiltar Sabon Gari, Aminu Abdullahi-Shagali, AbdulWahab Idris dake wakiltar Ikara, Yusuf Salihu dake wakiltar Kawo da Nasiru Usman dake wakiltar Tudun Wada.
Idan ba a manta ba a ranar 11 ga watan Yuli ne Mambobin majalisar dokokin jihar Kaduna 24 karkashin jagorancin shugaban majalisar, Yusuf Zailani suka tsige mataimakin shugaban majalisar Mukhtar Hazo.
‘Yan majalisar sun kalubalanci salon mulkin mataimakin shugaban majalisar da hakan yasa suka tsige shi.
Jim kadan bayan ambata tsige mataimakin shugaban majalisar sai aka nada Isaac Zankai dake wakiltar karamar hukumar Kajuru a majalisar sabon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar.
Bayan haka ‘yan majalisan da basu gamsu da nadin sabon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar ba sai dambe ya kaure a tsakani. An yayyaga riguna wasu kuma sun sha duka, babu kisa amma dai an yi tirmi.
Discussion about this post