Babban Bankin Najeriya, CBN, ya fito da kwararan matakan kwato bashi daga masu cin bashin bankuna su na kin biya da masu yi wa bankuna taurin-bashi.
CBN ya kirkiro wannan tsari a bisa Dokar Sashe na 2(d) na Dokar CBN ta 2007.
Kuma ya samu rattabawar Kwamitin Bankunan Najeriya baki daya, tun a ranar 18 Ga Fabrairu, 2020.
Tsarin ya fara aiki tun daga Asabar, 1 Agusta, 2020.
Za a fara bibiyar dukkan basukan da wa’adin biyan su ya wuce tun daga 28 Agusta, 2019.
Ga Tsauranan Matakan Masu Yi Wa Bankuna Taurin-bashi:
1. Daga 1 Ga Agusta, 2020 duk wanda ya rike wa banki ko bankuna kudi fiye da wucewar wa’adin biyan lamunin, ba zai sake yin mu’amala a kowane banki ba, sai ya biya bashin da wancan bankin ke bin sa rukunna.
2. Tsarin mai suna GSI, zai amince wa bankin da ya bayar da bashi ya karbo kudin sa daga asusun da mai taurin bashin ya ajiye kudade a wani banki.
3. Tsarin zai yi maganin masu karbar lamuni ko bashi daga bankuna su yi mirsisi su ki biya, ko kuma masu taurin-bashin da ke kin biyan banki kudin sa har a yi ta jekala-jekalar shari’a.
4. Tsarin zai rika sa-ido kan inda duk wadanda masu taurin-bashin banki ke karkatar da kudaden su cikin wani asusu daban.
5. Duk mai taurin bashin banki da mai ci ba ya biya, to ya yi shirin matsin-lambar biyan masu kudi kudaden su. Domin babu tsimi babu dabara, sai fa ya biya.
6. MISALI: Idan ka na da asusu a Guaranty Trust Bank, kuma ka ci bashin su ka ki biya, ka ma daina ajiya a bankin, to ga yadda za a kwaci kudin su daga bankunan Zenith Bank, Access Bank ko First Bank da ke ajiyar kudi a can.
7. Lambar Ajiyar Banki ta Sirri (BVN) din ka za ta nuna yawan asusun ajiyar da ka ke da su day yawan kudsden da ka ajiye.
8. Sai GT Bank ya tuntubi bankin da ka ke ajiya, a duba a tababtar kudaden ka da ke can ajiye a misali Zenith Bank, za su biya bashin da GT Bank ke bin ka, idan za su iya biya sai a kwashe kudaden a tura wa GT Bank.
9. Ko asusun hada-ka (joint account) aka samu da sunan ka a cikin masu ajiyar, to za a debi adadin da banki ke bin ka, a tura a bankin da ke bin ka bashin.
10. Ko wani ya turo kudi a asusun ka, matsayin aike ka kai wa wani kudin ko ka sayo masa wani abu, to bankin da ka zuba kudin zai kwashe ya tura wa bankin da ke bin ka bashi adadin da ake bin ka bashi ka ki biya.
11. Ba ruwan banki da irin asusun ajiyar ka. Ko ‘savings’ ko ‘current’ ne, duk wanda aka samu kudi a ciki a wani banki, za a kwashe a biya wancan banki da ke bin ka bashi.
12. Dama bankuna sun makala lambar BVN din ka a kwamfuta. Ko ba ka da ko sisi a Access Bank, duk ranar da kudi suka shiga a ciki, to idan First Bank na bin ka bashi, za a kwashi adadin abin da ake bin ka a tura wa First Bank kudin sa.
13. Idan aka ciri kudin mutum a bisa kuskure, to za a gaggauta maida masa kudin sa. Matsawar an tabbatar ba shi ne ake bin bashin kudaden ba.
14. Tsarin ya tanadi hukuncin tara daga naira 100,000 har zuwa milyan 10 ga inda aka samu tankiya, daukar tsawon lokaci ko tabka shari’a a kotu.
15. Hukuncin kan iya hawa kan wanda ake bi bashin ko kuma bankin da ya yi Ikirarin ya na bin wani bashi, amma husuma ta kai su a kotu har aka yi galaba a kan bankin. Ko kuma bankin ya yi galaba a kan mai taurin bashin.
Discussion about this post