Makusancin Mamman Daura, ya bayyana takamaimen dalilin fitar Mamman Daura zuwa London a ranar Talatar da ta gabata.
Aminu Balele-Kurfi, ya ce Mamman Daura wanda dan uwan Shugaba Muhammdu Buhari ne, ya tafi Landan domin a duba lafiyar sa, kamar yadda ya kan yi akai-akai.
Kurfi na maida raddi ne dangane da wasu rahotannin da ke cewa Mamman Daura ya garzaya Landan, saboda da wata rashin lafiyar da ake tunanin cutar Korona ce.
A tattaunawar da ya yi da PREMIUM TIMES, Aminu Kurfi ya ce, “duk duniya ta ga Mamman Daura lafiyar sa garas, babu alamar wani ciwo ko rashin lafiya a jikin sa, a lokacin da ya tafi Ingila ranar Talata.
“Domin kafin tafiyar sa, sai ma da ya halarci jana’izar marigayi Wada Maida tukunna. Kuma dama a Landan likitan sa ya ke, ya kan je a duba shi akai-akai.
“Da ni cikin wadanda suka raka shi filin jirgin sama a lokacin da ya tafi. Kuma su na sauka sai da ya kira ni, ya ce min sun sauka lafiya. Yau din nan Laraba ma sai da ya kira ni muka yi magana.”
Aminu ya ce masu yada labaran kanzon-kuregen cewa rashin lafiya ce mai tsanani ke damun Mamman Daura, karya suke yi.
“Ya kamata su sani cewa shekarun sa 80 a duniya. Don haka mai wadannan shekaru da yawa na da bukatar yawan ganin likitan sa akai-akai.” Inji Kurfi.
Ya ce masu watsa maganganun da ba daidai ba kan Mamman Daura na yi ne don saboda ya bayyana ra’ayin sa game da shugabancin Najeriya a 2023.
Kurfi ya ce Mamman Daura ya bayyana ra’ayin cewa cancanta za a bi a 2023, ba tsarin karba-karba ba.
“Mene ne laifi don mutum ya ce a bi cancanta a zabe ba karba-karba ba. A kudin din ma ai akwai wadanda suka cancanta sosai.
“Nan wasu suka rika hauragiya cewa a yi juyin juya-hali. Suka shiga zabe, jama’a suka guje su, hatta mazabar sa ko karamar hukumar sa ma bai yi nassra ba.