Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Wadata Manoma da takin zamani, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa dakatar da sarrafa sinadarin ‘urea’ ne ya sa manoma a kasar nan ke shan wahalar samun isasshen takin zamani.
Badaru wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Jigawa, ya ce gagarimin aikin raba taki kowane lungun kasar nan ya samu cikas ne saboda tsaida sarrafa sinadarin ‘urea’ da aka yi, sakamakon barkewar cutar Coronavirus.
Badaru ya yi wannan bayani a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, lokacin da ya ke hira da manema labarai.
Ya kara da cewa an dakatar da aikin samar da ‘urea’ ne bayan da aka samu bullar cutar Coronavirus a masana’antar, har ma cutar ta kama wasu ma’aikatan samar da ‘urea’ din.
Ya ce an rufe masana’antar Indorama mai samar da sinadarin takin urea bayan da aka samu wasu ma’aikata dauke da cutar Coronavirus. Sannan kuma dokar hana zirga-zirgar ababen hawa ma ta kawo cikas din zirga-zirgar dakon takin a loda shi a manyan motoci su na rarrabawa.
Bayan wannan dalilin, wasu dalilai da Badaru ya kara bayarwa su ne yadda manoma suka firgita suka banka kasuwanni suna sayen takin a lokaci guda su na boyewa a lokacin Korona.
Ya ce a lokacin su kuma masu saye su kimshe, su boye su na kara masa farashi, suka rika boyewa domin ya yi tsadar gaske, sannan su sayar.
Sai dai kuma yanzu ya ce duk an magance wadannan matsaloli da kalubalen da aka fuskanta.
Ya ce yanzu ana ta sarrafa takin, kuma Kwamitin Shugaban Kasa kan Wadata Manoma da Takin Zamani su na tura taki mai tarin yawa a masana’antu 31 na takin zamani a kasar nan domin ya wadaci manoma.
Yayin da ya ce an kama masu buga takin zamani na jabu, Badaru ya ce takin zamani wanda gwamnatin tarayya ke samarwa shi ne MPK 20:10:10, ba wani samfurin taki daban ba.
Ya ce idan sauran takin zamani sun yi karanci a kasuwa, to hakan na nufin mabukata ne ke yawan saye wanda ake kaiwa kasuwar kenan.