Dalilan da suka sa Kungiyar Lauyoyi ke kyamar El-Rufai ya halarci gagarimin taron su

0

Lauyoyin Najeriya masu tarin yawa sun rubuta sunayen su a wata rajistar wadanda ba su yarda Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya halarci gagarimin taron su na kasa, na shekara-shekara ba.

Tun da farko dai gwamnan ya na cikin wadanda Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) ta gayyata a matsayin Bakon Na Musamman Mai Jawabi, a taron wanda za a yi daga ranar 26 zuwa 29 Ga Agusta.

Manyan masu jawabai na musamman za su yi gurugubjin tattaunawa ne a kan: “Wane Ne Dan Najeriya?” Wato wata gogayyar wasa kwakwalce aka shirya yi a kwanaki ukun taron a kan tabbatar zama cikakken dan Najeriya.

Sauran wadanda za su yi jawabi a wudmrin har da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Gwamna Nyesom Wike na Ribas, Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila da Cif Jiojin Najeriya, Tanko Muhammad.

Akwai Olusegun Obasanjo da Ministan Shari’a, Abubakar Malami da sauran su.

Wannan ne taro na shekara-shekara na 60 da Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya ta shirya.

Rugugin Muryoyin Lauyoyin Da Ke Kyamar El-Rufai:

Mutunci Madara Ne:

“Idan wannan kungiya ta lauyoyi na da kima da ganin mutuncin kan ta da ganin kimar ka’idojin bin doka da turbar shari’a, to a cikin yini daya da tuni an rubuta wa Gwamnan Kaduna wasika, a sanar da shi cewa an fasa gayyatar sa, an maye sunan sa na babban bako jawabi da wani babban Bakon daban.” Inji Lauya Godwin Odimabo, da ke harka lauyanci a Fatakwal.

Idan Kudi Ya Biya Don Ya Yi Jawabi, A Mayar Masa Da Kudin Sa – M. M. Obono

“Idan kudi El-Rufai ya biya don ya zo ya yi jawabi a taron mu, to mu maida masa kudin sa. Idan kuma mu muka biya shi kudi, domin ya zo ya yi jawabi a taron na mu, to sai mu sanar da shi cewa mun janye, saboda wasu dabi’un da ya nuna, wadanda ba su yi tarayya da irin ra’ayoyin mu ba.”

Da ‘Mai Sheke Jinin Mutane’ Gara ‘Dan Giya’ -Lauya Nnamdi

“Ina alfahari da wadannan lauyoyi na cikin kungiyar mu. Na gode kwarai ganin cewa da yawan mu an yi barazanar kaurace wa taron muddin El-Rufai ya halarta. Shi dai ‘ita dai mashaya ai gidan mashaya giya ne, ba gidan masu kwana da kishirwar shan jinainan jama’a ba.”

“Ba Mu Kaunar Ganin Gwamnan Sansanin ‘Yan Kisan Kiyashi A Taron Mu” -Lauya Lugard

“Ni ma na shiga sahun abokan aiki na wajen yin tir da gayyatar da aka yi wa Gwamna El-Rufai na Kaduna. Gwamnan Kaduna, sansanin ‘yan kisan kiyashi”.

“Hanyar Jirgi Da Ban, Ta Mota Da Ban” – BNKY (Buka)

Babu ruwan El-Rufai da halartar taron Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya. Mutum ne da bai san darajar doka da oda da kiyaye mutuncin shari’a ba. Kotu ta sha samun sa da laifin kama mutane ya na garkamewa. Saboda haka tunda aka gayyace shi, ni na fasa zuwa taron.”

Haka lauyoyi da daa suka rika rubuta bakaken maganganu kan El-Rufai, tare da sanarwar fasa halartar taron. Sannan kuma su na neman a soke gayyatar da aka yi masa.

Sauran Dalilai:

1. Rashin nuna tausayi da alhinin kashe-kashen da ake yi a Jihar Kaduna.

2. Ikirarin da ya yi a lokacin zaben 2019, inda ya ce idan ‘yan kasar waje suka tsoma baki a zaben Najeriya, za a maida gawarwakin su a kasashen da suka fito a cikin ‘makara’.

3. Barazanar da Dan sa Bello ya yi cewa zai iya tirmishe wata matar aure, ya yi mata fyade.

4. Yawan kama masu adawa da El-Rufai ke yi ya na garkamewa.

Shugabannin gungun wadanda ba su yarda a gayyaci El-Rufai ba, sun ce ko a cikin lauyoyi ma El-Rufai ya muzguna wasun su.

“Lokacin da mambobin mu ke fama da gallazawar wulakancin El-Rufai, Kungiyar Lauyoyi ta Kasa babu wani kokari ko hobbasa da ta yi. To idan ka ce lauyoyi su goyi bayan halartar El-Rufai, ranar da giyar mulkin sa ta motsa ya hau ta kan su kuma fa. Wane kokari za ka yi!”

Silas ya ce ko a wurin taron 2018, an tafka kuskure, yayin da aka bai wa Shugaba Muhammadu Buhari dama ya je ya yi kamfen din sa da sunan jawabi a wurin taron.

Hakan kuwa a cewar Silas, ya kauce wa akidar Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya.

Ya zuwa ranar Laraba dai har an samu lauya 700 daga cikin 1000 da ake so su yi rajistar korafin rashin amincewa da halartar El-Rufai. Ko kuma su su amince za su kaurace idan El-Rufai ya halarta.

Share.

game da Author