Daliban Najeriya da ke karatu a kasar Cyprus, wato TRCN sun karyata Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), da ta gargadi iyayesu daina tura ‘ya’yan su Arewacin Cyprus, ta ce ana yi masu fyadar-‘ya’yan-kadaya.
A ranar Litinin ce Abike Dabiri-Erewa ta yi wannan gargadin cewa ana kashe daruruwan ‘yan Najeriya a Arewacin Cyprus, ba tare da gwamnatin kasar ta yi kwakkwaran bincike ba.
Dabiri ta yi wannan ikirari bayan an samu labarin kisan wani dalibi mai suna Ibrahim Khaleel.
Dalibin wanda dan Najeriya ne, an kashe shi kuma har yau ba a ji wani karin bayani ba.
“Kisan da aka yi wa Ibrahim Khaleel zai zama darasi ga iyaye su daina tura yaran su a duniya, ana kashe su a banza., musamman a kasar Arewacin Cyprus.”
“Matsalar ita ce mutane ba su san cewa duk duniya ba a yarda akwai kasar Cyprus ta Arewa ba. Majalisar Dinkin Duniya ma ba ta amince da Kasar ba.
“Amma dubban ‘yan Najeriya na zaune a kasar su na karatu, amma sai kashe daruruwan ‘yan Najeriya a ake yi a kasar.
Dabiri har cewa ta yi Najeriya za ta bayyana sunayen daruruwan ‘yan Najeriya da aka yi wa kisan gilla a kasar.
Sai dai kuma yayin da suke maida mata martani, daliban Najeriya da ke karatu a kasar ta ce, “Zaman lafiya a kasar Cyprus ta Arewa, ya fi na Najeriya, nesa ba kusa ba.
Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya Masu Karatu Kasashen Waje (NANS), Evidence Akhayere, ya ce duk da dai ‘yan Najeriya masu karatu a kasashe su na fuskantar kalubale, to masu Karatu a Arewacin Cyprus ba su fama da matsala, kalubale ko wata tsangwama.
Haka Evidence ya shaida wa PREMIUM TIMES a ‘yar tattaunawar da suka yi.
Ya ce ba gaskiya ba ne da ta ce daruruwan daliban Najeriya sun mutu a Cyprus. Ya ce maganar mutuwar dalibi 100 karya. Kalilan da suka rasu duk ciwon ajali ne, ba kisan-gilla ba.