DAKATAR DA EL-RUFAI DAGA HALARTAR TARON NBA: Nuna bangaranci da kiyayya ne daga wasu tsiraru, Daga Mohammed Mohammed

0

Abinda ya tada min da hankali a cikin kwanaki biyu da suka gabata bai wuce yadda wasu tsirarun ‘yan kungiyar Lauyoyin Najeriya sukai ruwa sukai tsaki sai an cire gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai daga cikin jerin wadanda za su yi jawabi a taron kungiyar na shekara-shekara.

Tabbas kowa yana da ikon bayyana ra’ayinsa a ko da yaushe amma ra’ayin wasu tsiraru bai isa a ce an hargitsa tsarin taro na kungiya da ya shafi duka ‘yan kasa Najeriya ba.

Wannan kungiya ta lauyoyi ba kungiya bace ta ‘yan kudu ko kuma wani yanki a kasar nan. Kungiya ce ta duk ‘yan Najeriya da dole kowa dake kasar nan kuma mamban wannan kungiya na da iko ya ce ga abinda ya ke so.

Idan wasu tsiraru za su hayayyake su tada jijiyoyin wuya kan wani da ba su so ya halarci taro na kasa haka sannan uwar kungiya ta biye musu ta bi abinda suke so, ashe kowa ma zai iya zakalkalewa akan wani da ba ya so kuma a bi abinda ya ke so.

Shawarar da kungiyar Lauyoyi ta Kasa ta dauka na cire sunan El-Rufai daga cikin wadanda za su yi jawabi a wannan taro nuna bangaranci ne, nuna kiyayyace sannan kuma da kawo rudani a cikin wannan kungiya.

Masu korafi sun yi zargin nuna halin ko in kula da yadda El-Rufai ke kokarin kawo karshen rashin zaman lafiya a yankin Kudancin Kaduna.

Wannan abu ba daidai bane kuma ba gaskiya bane. Babu wani mazaunin Kaduna da bai san yadda gwamnan ya maida hankali wajen ganin an kawo karshen kisan da ake ya a jihar baki daya ba.

Kamar yadda ya ke a jihar, ba yankin kudancin Kaduna ba ne kawai yan ta’adda suke kai hare-hare. Yankunan Birnin Gwari, Igabi, Giwa da Kajuru duk da suke yankin Kaduna ta tsakiya sun fi fama da ayyukan ‘ta’addanci da hare-hare amma da ya ke ba sune damuwar mutane ba musamman mazauna kudancin Najeriya, sai idan an kashe dan kudancin Kaduna ne kawai shi kenan babu tsaro a Kaduna.

Hare-haren ‘yan ta’adda da mahara abu ne da ake fama da shi a yankin Arewa gaba daya.

Amma kuma sai wasu suka tsame yankin kudancin Kaduna, idan aka kashe mutum daya shikenan, gwamnati bata komai akan tsaro, idan kuma su ne suka kashe, babu komai sai kaji an yi shiru tsit.

A wannan taro na kungiyar Lauyoyi, har da gwamnan Ribas, wanda kowa ya san yadda yake. Ammam kuma wai har shine ya fi daraja fiye da El-Rufai a wajen tsirarun ‘ya’yan kungiyar.

Share.

game da Author