Reshen kungiyar Lauyoyi ta jihar Jigawa ta yi kira da kakkausar murya ga shugabannin kungiyar ta Kasa, da ta janye shawarar ta da dakatar da El-Rufai daga yin jawabi a Taron kungiyar ta Kasa.
Shugaban Kungiyar Lauyoyi na reshen jihar Jigawa Garba Abubakar, ya ce shawarar cire El-Rufai daga masu jawabi a taron bai dace ba kuma nuna bangaranci ne a kasar nan.
” Wannan taro ba na wani yanki bane ko kuma na wasu mutane kalilan a fadin kasar nan. Wannan kungiya na duka ‘yan Najeriya ne sannan abinda ake zargin sa da shi, ba a bashi damar kare kan sa ba. Kawai don wasu sun ce basu so sai ace kungiya ta yanke shawarar haka.
” Idan har za a iya baiwa gwamnan Ribas, Nyesom Wike damar yin jawabi a taron, bamu ga dalilin da zai sa ace wai an hana Nasir El-Rufai ba. Kowa ya san yadda Wike yake mulkin kamakarya a jihar sa. Ya rusa gidaje, wuraren ibada kuma ba wanda ya isa ya ce masa Kala. Amma kuma wai shi an bashi dama.
Kungiyar tace ko aba Nasir El-rufai dama yayi jawabi ko kuma ta ki halartar taron.
Wasu tsirarun mambobin kungiyar lauyoyi sun nemi a dakatar da El-Rufai daga halarta da yin jawabi a taron kungiyar ta Kasa da za a yi a a makon gobe.
Hakan yayi tasiri bayan korafi da suka rika yi, har uwar kungiyar ta cire sunan El-Rufai a cikin jerin sunayen wadanda za su yi jawabi a taron.
Shi ko El-Rufai, ya maida wa kungiyar martani yana mai cewa ko da su ko basu, zai ci gaba da fadin gaskiya a duka lokacin da ya samu damar haka.