Babban Bankin Najeriya (CBN), ya hana kamfanonin saida wutar lantarki (Discos) karbar kudaden wuta ya maida aikin karbar kudaden a hannun bankuna.
Daraktan Kula da Bankuna, Hassan Bello ne ya bayyana haka, tare da cewa kwamitin lura da harkokin lantarki na kasa ne ya cimma wannan matsaya, domin a kauce dimbin matsalolin da aka rika fuskanta wajen tara kudaden.
Sanarwar ta ce daga yanzu za a rika biyan kudin wuta ne kai-tsaye a bankuna, daga nan sai banki ya biya kamfanonin saida wa jama’a wutar lantarki. Kuma banki zai biya Hukumar Raba Wutar Lantarki na ta kudin kai-tsaye.
Sanarwar ta hana kamfanonin saida wuta Discos karbar kudaden wuta ko wasu kudaden harkokin lantarki na Discos din.
CBN ya jaddada cewa asusu ne za a bude mallakin Hukumar Kula Da Hasken Lantarki ta Kasa, Hukumar Rarraba Hasken Lantarki ta Kasa da kuma Kamfanonin Saida Wutar Lantarki (Discos) su 11 da ake da su a kasar nan.
CBN ya ce ana kwana ana tashi kullum Discos na fuskatar matsalar karbar kudaden wuta. Shi ya da bashin da Discos din ke karba ya yi yawa matuka.
Takardun bayanai sun tabbatar ana bin kamfanonin saida wuta (Discos) su 11 bashin naira bilyan 622. Sai kuma kudin ruwan da suka rika taruwa, har a yanzu suka kai naira bilyan 308.
Yanayin harkar wutar lantarki ya shiga jula-jula a kasar nan, yayin da su ma kamfanonin Discos masu raba wuta ke kukan cewa kwastomomi da dama ba biyan kudin wuta su ke yi ba, saboda yawanci idan ba a manyan birane ba, ba a amfani da mita.
Kwastomomi na kukan cewa ana yi musu aringizon kudaden wuta, kuma idan sun tambayi mita ba su samu da wuri.