CIYAR DA YARAN MAKARANTA: Gwamnatin Kaduna na tantance masu dafa abinci

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara tantance masu dafa wa yaran makarantar 7,261 abinci domin tsaftace shirin bayan samun matsaloli da aka yi a baya.

Jami’in shirin ciyar da yaran makaranta abinci na jihar Kaduna, Umar Abdullahi ya sanar da haka a wani taron bita da yin garambauwaul ga wannan shiri da aka yi a Zariya.

Abdullahi ya ce an yi wannan Zama ne domin tattauna matsalolin da masu dafa abinci kan fuskanta da suka hada da yadda ake dafa abincin, yadda ake biyan su kudaden su da ingancin abincin da ake dafawa.

Bayan haka jami’an gwamnati sun bi dadalla-dalla irin abincin da ake dafawa yaran makaranta daga litini zuwa juma’a.

Abdullahi ya ce ana ciyar da yaran makaranta 735,280 a makarantu 3,449 a kananan hukumomin jihar.

Sannan kuma gwamnati ta tallafa wa iyayen yaran makaranta a lokacin Korona da kayan abinci a jihar.

An raba wa gidadje 2500 kananan buhunan shinkafa, wake mangyada, manja gishiri da Maggi.

Idan ba a manta ba jihar Kaduna ce ta fara ciyar da yaran Makaranta a binci kyauta a kasar nan, kafain gwamnatin tarayya ta ci gaba bayan jihar ta dakatar.

Hakan ya sa an samu karin yaran makaranta a jihar bayaga aikin gyaran makaruntun da gwamnati ta maida hankali a kai.

Share.

game da Author