Cikin watanni bakwai da fara bayyanar cutar, Coronavirus ta kama sama da mutum milyan 20 a duniya, kamar yadda rumbun adana alkaluman kididdigai adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus mai suna worldometers.info ya bayyana, a ranar Lahadi da daren da ya gabata.
An samu adadin na sama da mutum milyan 20, watanni biyar bayan Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa Coronavirus ta tashi daga cuta ta zama mummunar annobar da za ta buwayi duniya baki daya.
A wancan lokaci kuwa, wadanda suka kamu da cutar a ranar 11 Ga Maris, su 118,000 ne a duniya.
Ya zuwa 1 Ga Afrilu kuwa, cutar Coronavirus ta kama mutum milyan 1.
Zuwa 10 Ga Yuli, cutar Coronavirus ta kama mutum milyan 10 a duniya.
Korona ta yi mummunar illa a Turai da Amurka da Kudu maso Gabacin Asiya sai kuma ysnzu da ta darkaki Afrika da Latin Amurka gadan-gadan.
Har yanzu dai babu rigakafin hana kamuwa da cutar Coronavirus ko maganin warkar da ita kaifi-daya.
Zuwa ranar Lahadi da dare, mutum milyan 20, 055, 099 ne suka kamu a fadin duniya.
Makonni biyu da suka gabata, PREMIUM TIMES ta kawo rahoto dalla-dalla kan yadda Korona ta kama sama da mutum milyan 16, ta kashe 650,000 a duniya.
Kenan cikin makonni biyu zuwa Lahadin da ta gabata, cutar Coronavirus ta kara kama sama da mutum milyan 4 kenan a duniya.
Duk da irin wannan fantsama da annobar Korona ke yi tare da kisa a duniya, akwai milyoyin mutane har a nan Najeriya da ba su yi amanna cewa akwai cutar ba.
Yadda Korona ta Kama Sama Da Mutum Milyan 16 Cikin Wata 7:
1. Makonni 15 bayan farkon bullar cutar, adadin wadanda suka kamu a duniya sun kai mutum milyan 2.
2. Zuwa ranar 13 Ga Yuli, ta kama mutum milyan 13 a duniya.
3. Kwanaki 5 bayan adadin ya kai milyan 13, ta kara kama mutum milyan 2, yadda adadin ya haura mutum milyan 15 a ranar 21 Ga Yuli.
4. Zuwa rubuta wannan labari, mutum milyan 16, 202,385 suka kamu a duniya.
5. Wadanda cutar ta kashe zuwa wannan rana sun kai mutum 650,000.
6. Korona ta fi yin mummunar illa a kasashe hudu na duniya: Amurka, Brazil, Rasha da Indiya.
7. Korona ta kama mutum milyan 4, 315,709 a Amurka; sama da mutum milyan 2.3 a Brazil, mutum 806, 720 a Rasha, sai mutum sama da milyan 1 a Indiya.
8. Mutum milyan 9 da cutar ta kama daga milyan 16 da Korona ta kama da duniya, duk a kasashen Amurka, Barazil da China suke. Kusan rabin wadanda ta kama a duniya kenan.
9. Korona ta kama mutum 40,000 a ranar Juma’a, a kasar Indiya a rana daya kenan.
10. Mutum milyan 9, 919,232 suka murmure bayan Korona ta kwantar da su a duniya.
11. Sama da mutum 800,000 Korona ta kama a Afrika.
12. Korona ta kashe sama da mutum 17,000 a Afrika baki-daya.
A Afrika ta Kudu Korona ta fi yin mummunar illa a nahiyar Afrika. Mutum 432, 200 suka kamu, a cikin su ta kashe mutum 6,655.